Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Honarabul Yusuf Zailani, ya ce majalisar dokokin jihar ba ta da wani shiri na tsige gwamna Nasir El-Rufai.
Da yammacin ranar Asabar ne rahotanni suka bayyana a kafafen sada zumunta cewa majalisar dokokin jihar ta fara yunkurin tsige gwamna El-Rufai bisa zargin cin hanci da rashawa.
- Ra’ayoyinku A Kan Hauhawar Farashin Kayan Masarufi
- Da Dumi-Dumi: ‘Yansanda Sun Cafke Wani Dan Bindiga Dan Shekara 20 A Kaduna
Sai dai kuma Hon. Ibrahim Dahiru Danfulani, hadimin kakakin majalisar kan kafafen yada labarai, a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, ya bayyana cewa rahotannin na ‘yan adawa ne da makiya ci gaban alakar da ke tsakanin bangaren majalisar dokoki da na zartaswa karkashin jagorancin Malam Nasiru El-Rufai.
Ya ce bisa ga dukkan alamu an fitar da rahoton karya ne domin haifar da rikici tsakanin ‘yan majalisa da na zartaswa da kuma hana al’ummar Jihar Kaduna cin ribar dimokuradiyyar da suke amfana.
“Rahoton wanda ya kuma ce dangantakar da ke tsakanin gwamnan da kakakin majalisar dokokin Jihar Kaduna, Rt. Honorabul Yusuf Zailani, ba komai ba ne illa karya” inji sanarwar.
Sanarwar ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne maganar da ake yi cewa a halin yanzu ‘yan majalisar dokokin jihar na binciken yadda aka kashe wasu kudade na ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar ta yi.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, dukkan rahoton an hada su ne da mugun nufi domin a kawo rudani a zukatan jama’a, don haka sun bukaci a yi watsi da shi baki daya.
A cewar sanarwar, za a yi nazari sosai kan asalin rahoton da aka ce ya fito da nufin gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika da masu daukar nauyinsu domin ya zama izina ga na baya.
Ya kuma kara tabbatar da cewa alakar da ke tsakanin majalisar da ta zartaswa tana da inganci.