Biyo bayan barazanar daukar matakin shari’a, sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a Jihar Kwara, Prince Tunji Moronfoye, ya janye zargin cewa gwamnan jihar, AbdulRahaman AbdulRazaq, ya bai wa kwamishinan zabe na jihar, Mal. Garba Attahiru Madami, miliyan 300 domin murde zaben gwamnan jihar a 2023.
Moronfoye, a wata sanarwa da ya fitar a Ilorin, babban birnin jihar a ranar Talata, ya mika uzuri ga gwamna da kuma REC, inda ya ce zarginsa “a gaskiya yaudara ne da rashin tabbas, musamman ma inda na bayyana cewa kudi miliyan 300 sun yi batan dabo”.
- Dan Takarar Gwamnan Katsina A NNPP Ya Ba Da Tallafin Miliyan 50 Ga ‘Yan Gudun Hijira
- Adamu Yaki Cewa Uffan Kan Mika Sunan Lawan Da Akpabio Ga INEC
Madami, a ranar Litinin din da ta gabata ta bukaci jam’iyyar PDP “ta ba da uzuri a hukumance cikin sa’o’i 48, bisa zargin bata kudin.”
REC ta kara da cewa zai nemi hakkinsa a gaban kotu idan jam’iyyar ta ki yin uzuri a kafafen yada labarai cikin sa’o’i 48 daga ranar Litinin.
“Ina bai wa PDP sa’o’i 48 don neman afuwar jama’a kan rubuce-rubuce a kafofin watsa labarai, wanda bayan karewar wa’adin, zan dauki matakin shari’a kan bata suna da mutuncina.”
Bayanin da Moronfoye ya bayar na janye zargin da ba a tabbatar da shi ba kan Gwamna AbdulRazaq da kuma REC yana cewa: “Ni, Prince Tunji Moronfoye, sakataren yada labarai na PDP na janye sanarwar manema labarai kan kalamai na.
“An gano wannan babban kuskure ne bayan bincike mai zurfi kan bayanan da aka fitar, ina neman afuwar Malam AbdulRahman AbdulRazaq, gwamnan jihar Kwara da Malam Garba Attahiru Madami, kwamishinan zabe na jihar Kwara kan wannan batun dama yi.
“Ina kuma neman afuwar kowa, kan rashin jin dadi da kalamai na ya haifar da furucina.”