ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zargin Daura Aure Da Mai Kanjamau: Yadda Aka Tube Hakimi A Katsina

by Yusuf Shuaibu and El-Zaharadeen Umar
3 years ago
Kanjamau

Hakimin Kuraye da ke karamar hukumar Charanchi a Jihar Katsina, Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu, ya mayar da martani kan zargin da masarautar Katsina ta yi masa na yin murabus.

Idan za a iya tunawa dai wata sanarwa da masarautar ta fitar ta ce an kwace masa sarautar Sarkin Kurayen Katsina bisa umarnin Gwamnatin Jihar Katsina.

  • Bunkasa Kimiyya Da Fasaha: Nijeriya Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasar Cuba

Sai dai kuma a wata sanarwa da daraktan yada labarai na sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Aliyu Yar’adua ya fitar ya ce an tilasta masa yin murabus ne ba bisa shawarar masarautar Katsina ba.

ADVERTISEMENT

Da yake mayar da martani game da lamarin ta wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, Alhaji Ahmadu ya ce, “Ba da son raina na amsa wasiku guda biyu da ke dauke da ranar 18 ga watan Satumba 2023, wadanda suka yi ta yawo a kan cewa na yi murabus daga mukamin Hakimin Kuraye.
“Wasikar farko ta zo ne daga majalisar masarautar Katsina, wadda a bangare guda ta bayyana cewa na yi murabus bisa ga umarnin da gwamnatin jihar ta ba ni.

“Wasika ta biyu ta kasance ne kamar wata sanarwar manema labarai da daraktan yada labarai na gwamnatin jihar ya fitar, inda ta bayyana cewa na yi murabus bisa amincewar shawarar da masarautar Katsina ta ba ni a kan wani laifin da ake zargi na da shi na gudanar da wani daurin aure ba tare da takardar shaidar likita ba, inda ya bayyana daya daga cikin ma’auratan yana dauke da kwayar cutar kanjamau.

LABARAI MASU NASABA

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

“Tare da mutuntawa, gwamnati da majalisar masarautu da alama suna zargin juna, duk da cewa takardar koken ya samu asali ne daga gwamnatin jihar ba masarautar da nake aiki da ita ba a matsayin Hakimi.”
Basaraken ya kara da cewa, hakika mutanen biyu da ake magana a kai (ma’auratan) sun tuntube shi domin ya jagoranci aurensu.

Ya bayyana cewa kamar yadda dokar ta tanada kan nuna kyama ga masu dauke da cutar kanjamau, ya kai su wurin likitan, inda daga bisani kuma ya kai su wurin hukumar yaki da cutar kanjamau ta jihar (SACA).

“An ba su shawarar da ta dace game da wannan auren kuma dukkansu sun amince da su bi ka’idoji suka shimfida. A irin wannan yanayi sananne ne cewa idan mutum daya ko duka bangarorin biyu suna dauke da kwayar cutar kanjamau, doka ta hana nuna kyama da wariya ga duk wani batun takardar shaida daga likita.

“Dukkanin bayanan da suka shafi wannan lamari, da suka hada da wasikar yarjejeniya daga wurin mutumin, magungunan da likitan ya ba da shawarar, masu ba da shawara na SACA da yarjejeniyar sirri da aka gabatar ga gwamnatin jihar. A bari jama’ar da aka yi wa wannan rashin adalci su zama alkalai,” in ji shi.

Ba a dai bayyana ko an bai wa basaraken damar ba da nasa shaida kafin a yanke hukuncin ya yi murabis ko a’a.

Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin, Malam Dikko Umar Radda ta ba da umarnin cire rawanin Sarkin Kurayen Katsina Hakimin Kuraye a karamar hukumar Charanci bisa zarginsa da daura aure da mai cutar kanjamau.

Bayanin haka yana kunshe ne a cikin wasu takardun guda biya masu karo da juna wanda gwamnatin ta fitar da kuma masarautar Katsina.

Takardar farko da masarautar Katsina ta aike da korarar Hakimin wanda sakataren masarautar Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo ya sanya hannu ta bayyana cewa an yi wa sarkin Kurayen Katsina, Alhaji Abubakar Al’adu ritaya ne bisa umarni da masarautar ta samu daga ofishin sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Garba Faskari.

“Ta ce bisa umarni da muka samu daga ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Katsina mai lamba KTS/SGS/SEC.54/T/7 ta ranar 15 ga watan Satumbar 2023 a kan maganar daurin auran Alhaji Lawal Mamman Auta da Hajiya Halimatu Abdullahi Kuraye wanda haka tasa gwamnati ta ba da umarnin yi maka ritaya daga mukaminka.”

Sai sanarwar ta ci gaba da cewa bisa wancan umarni na gwamnatin Jihar Katsina masarautar Katsina ta yi wa sarkin Kurayen Katsina Hakimin Kuraye ritaya daga mukaminsa a ranar Litinin 18 ga Satumbar 2023.

Jim kadan bayan wancan sanarwar ta fadar mai martaba sarkin Katsina, sai kuma ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Katsina ya fitar da wata sanarwar ga manema labarai wanda daraktan yada labarai, Abdullahi Aliyu ya sanya wa hannu aka raba wa manema labarai a Katsina.

Sanarwar ta ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa bisa la’akari da shawarwarin masarautar Katsina gwamnati ta amince da yi wa sarkin Kurayen Katsina Hakimin Kuraye, Alhaji Abubakar Abdullahi Amadu ritaya daga mukaminsa na hakimi.

Haka kuma sanarwar ta ce hakan ya biyo bayan wani korafi ne da aka shigar wanda gwamnatin jihar ta amsa a kan tsohon Hakimin wanda kuma aka tura wa masarautar Katsina ta gudanar da bincike a kan tsohon Hakimin, sannan ta same shi da laifin yin jagorancin daura aure da mai dauke da cutar kanjamau.

Toni dai masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum suka fara tofa albarkacin bakinsu a kan wadannan takardu masu karo da juna, inda masautar Katsina ke kokarin wanke kanta da cewa umarni ta samu daga sama kafin yi wa hakimin ritaya, a yayin da gwamnatin Jihar Katsina ke cewa masarautar ce ta gudanar da bincike ta kama Hakimin da laifi kafin daukar matakin.

Sai dai kuma wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa korarar hakimin yana tsama da mai garin Kuraye wanda yake baban amini ga gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda wanda dukkan su ‘yan asalin karamar hukumar Charanci ne baki daya.

Kanjamau
Yusuf Shuaibu
+ posts Bio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Yadda Matsin Lamba Ta Sa Amaechi Ya Amince Ya Zama Abokin Takarar Atiku
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: Kallo Ya Koma Kan Yadda APC, ADC Da PDP Ke Neman Abokan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Kanjamau
El-Zaharadeen Umar
+ posts Bio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mutum 1,000 Daga Jam’iyyar ADC Sun Koma PDP A Jihar Katsina
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Amince Da Ɗaukar Ma’aikatan Gandun Daji 1,000 Domin Matsalolin Tsaro A Katsina
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Matsalar Tsaro:Yadda Sabbin Matakan Gwamnati Ke Shafar Walwalar Al’ummar Jihar Katsina
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

MASU ALAKA

Nijeriya
Rahotonni

An Nemi Shugabanni Su Rungumi Tafarkin Adalci A Tsakanin Al’ummunsu

June 20, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
Rahotonni

Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji

June 20, 2026
IMF
Rahotonni

Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF

June 20, 2026
Next Post
Xi Jinping Ya Bukaci A Raya Masana’antu Masu Inganci

Xi Jinping Ya Bukaci A Raya Masana'antu Masu Inganci

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

June 25, 2026
Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

Mukaddashiyar Shugaban Venezuela Ta Yi Godiya Da Aniyar Sin Ta Ba Su Agaji

June 25, 2026
Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

Shugabar Namibia Ta Kaddamar Da Dakin Baje Kolin Kimiyya Da Sinawa Suka Gina

June 25, 2026
Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara

June 25, 2026
Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta

June 25, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita

June 25, 2026
Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

June 25, 2026
Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

June 25, 2026
Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

June 25, 2026
Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

June 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.