Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da wani mai taimaka ma ta kan harkokin siyasa, Ibrahim Rabi’u, sakamakon fitar da wata sanarwa ta karya mai cike da cece-ku-ce da ake dangantawa da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shugaban jam’iyyar NNPP kan cewa, ya ki amincewa da tayin da shugaba Bola Tinubu ya yi masa na komawa jam’iyyar APC.
Sanarwar dakatarwar wacce ta fara aiki a ranar Asabar, 17 ga Mayu, 2025, ta fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Umar Farouk Ibrahim, sannan mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana.
- Wasu Kyawawan Ɗabi’u Da Suke Ƙarfafa Zamantakewar Aure
- Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta
A cewar sanarwar, Rabi’u, wanda ke aiki a matsayin babban mai ba da rahoto na musamman (SSR) a ma’aikatar sufuri, an dakatar da shi ne saboda “furucin da ya yi da sunan Kwankwaso kuma ba tare da izininsa ba”.
Gwamnati dai ta nisanta kanta daga labarin na karya, inda ta kwatanta batun da cewa, “mai tada hankali da rashin izini”.
Gwamnatin jihar ta kuma gargadi dukkan masu rike da mukaman siyasa da su daina bayyana ra’ayoyinsu da sunan Gwamnati kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi siyasa ba tare da tantancewa ba.
LEADERSHIP ta fahimto cewa, wannan matakin ya biyo bayan wani labari ne da aka yada da cewa, Sanata Kwankwaso ya ki amincewa da tayin da shugaba Tinubu ya yi masa na tsunduma shi cikin jam’iyyar APC, inda ake zargin Sanatan ya bayyana cewa, ya gwammace ya bar siyasa maimakon ya koma jam’iyya mai mulki.
Ba da dadewa ba, wannan labarin na karya ya samu karbuwa a shafukan sada zumunta wanda Kwankwaso da gwamnatin Kano, tuni suka yi martani a kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp