Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta ayyana cewa zargin kisan kai da hada kai wajen yin kisa da ake yi wa shugaban masu rinjaye na Majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa.
Da yake jagorantar hukunci kan bukatar da Doguwa ya shigar kan tauye masa hakki da ‘yanci da tsare shi ba bisa ka’ida ba da karamar kotu ta yi, Mai Shari’a Mohammed Yunusa, a ranar Litinin ya ce, babban Kotun Majistire ba ta da hurumin sauraron karar da ya shafi aikata manyan laifuka.
- Ba Ni Da Hurumin Gurfanar Da Alhassan Doguwa —Antoni-Janar
- Alhassan Ado Doguwa Ya Sake Lashe Zaben Dan Majalisar Wakilai A Kano
Mai Shari’a Yunusa ya buga misali da sashi na 251 (1) da ya ce babbar Kotun tarayya ce kadai ke da ikon sauraron karar da ta shafi bindigu kamar dai irin tuhumar da aka shigar kan Ado Doguwa.
Sai dai Alkalin ya nanata cewa ba fa kawai don an amince da bada belin Doguwa shi ke nan hakan na nuni da cewa ya samu kariyar da ba zai fuskanci shari’a ba ne, Yunusa ya ce dole a bi komai bisa doka da ka’ida.
Lauyan Ado Doguwa, Nureini Jimoh, shi ne ya nema masa umarnin samun kariya kan ‘yancin dan adamtaka kamar yadda dokar kasa ta bayar da dama ga kowa.
Lauyan nasa ya yi ikirarin cewa ‘yansanda sun tsare Doguwa ba bisa ka’ida ba wanda hakan ya taba masa hakkinsa da ‘yancinsa kamar yadda dokokin mulkin kasa na 1999 suka bayar.
Kazalika, ya bukaci kotun ta ayyana cewar sauraron karar da kotun Majistire ta yi bai dacewa ba kuma ajingine shi tare da ayyana cewar hakan ya saba wa tsarin mulkin kasa domin ba ta da hurumin da karfin ikon sauraron irin wannan karar da suka shafi manyan laifuka.
Alkali Yunusa ya ce ‘yan kasa na da dama bisa tanade-tanaden doka sashi na 46 (1) na kundin tsarin mulkin kasa ta 1999 da su je kowace babban kotu domin kalubalantar yunkurin tauye musu hakkinsu.
Mai Shari’a Yunusa ya ce tun da farko ma Bai dace a tsare Doguwa a gidan yari ba domin ba a gabatar da karar da ake masa ta hanyoyin da suka dace ba, ya kara da cewa shigar da karar da ‘yan sanda suka yi a karamar kotu bai dace ba.
Don haka ne ya haramta wa ‘yansanda kamawa, musgunawa ko tsare Alhassan Doguwa.