Ministar Al’adu, Hannatu Musawa ta bayyana cewa, zargin da ake mata na karya dokar kasa sam ba haka ba ne, inda ta ce “babu wata doka da na karya”.
Hannatu ta musanta zargin ne a ranar Lahadi cikin wani rahoto da ta fitar, inda ta kara da cewa “babu wata doka a kundun tsarin mulkin Nijeriya da ta ce, shugaban kasa ko wata hukuma, ba su da ikon nada wani ko wata da yake ko take hidimar kasa a mukamin siyasa.”
Hukumar kula da masu yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) ta tabbatar da cewa ministar al’adu, Hannatu Musawa tana cikin masu yi wa hidima kasa amma bata kammala ba.
Kungiyar Marubuta da ke kare Hakkokin Dan Adam ta Nijeriya (HURIWA) ce ta yi zargin, inda ta ce, Musawa na cikin masu yi wa hidima kasa (NYSC) bata kammala shirin ba, don haka ta taka dokar kasa.
HURIWA ta bukaci hukumar NYSC da ta tilasta Musawa ta zaba tsakanin hidimar kasa ko kuma nadin minista.