Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya musanta alaka da ‘yan bindiga a Jihar Zamfara, ya kuma kalubalanci Gwamna Dauda Lawal da wasu da su rantse da Alkur’ani mai tsarki don tabbatar da cewa, ba su da hannu kan ayyukan ta’addanci da ya addabi Jihar.
A baya-bayan nan ne, Gwamna Dauda Lawal ya soki Matawalle da cewa, yana da alaka da ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
- Wakilin Musamman Na Xi Jinping Ya Halarci Taron Tattauna Kan Makomar Duniya
- Ofishin Jakadancin Saudiyya Ya Yi Bikin Cikar Daularsu Shekaru 94 Tare Da Karfafa Alaka Da Nijeriya
Amma, Ministan kuma tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, yayin da yake magana a gidan Talabijin na Channels a ranar Talata, ya kuma kalubalanci ‘yan siyasa ciki har da Gwamna Lawal da su rantse da Alkur’ani mai girma don tabbatar da cewa, ba su da hannu a ta’addancin da ya addabi jihar Zamfara.
Ya ce: “Ni kadai ne gwamna da na rantse da Alkur’ani cewa, ba ni da wata alaka da ‘yan bindiga.
“Ina kalubalantar duk ‘yan siyasa da suka hada da Janar Ali Gusau da Dauda Lawal da su yi hakan. Babu daya daga cikinsu da zai iya yin rantsuwa, kuma idan ba su yi rantsuwar ba, hakan na nufin suna da hannu cikin rashin tsaro a jihar,” inji shi.
Idan dai za a iya tunawa, Gwamna Lawal ya bukaci ministan da ya yi murabus daga mukaminsa domin ya wanke sunansa, inda ya ce, tsohon gwamnan ya taba ajiye ‘yan ta’adda a gidan gwamnati da ke Gusau, babban birnin jihar, kuma gwamnati na biyan ‘yan ta’addan kudade.
Matawalle, ya kare matakin da ya dauka na tattaunawa da ‘yan bindiga a lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara, lamarin da ya ce, gwamnoni da dama sun goyi bayan tsarin, kuma ya kai ga ‘yantar da mutanen da aka sace tare da mika wa gwamnati makamansu a jihar.