• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zargin Tarkon Bashi Na Shan Suka Daga Sassan Afirka

by CMG Hausa
3 years ago
Tarkon bashi

Ga duk mai bibiyar kafafen watsa labaran yammacin duniya, da irin kalaman da kan fito daga bakunan manyan jamian Amurka, ba zai rasa jin zarge-zarge marasa dalili kan kasar Sin ba. Cikin wadanda suka fi fitowa fili, a baya bayan nan an ji zargin cewa wai kasar Sin na Danawa kasashen Afirka Tarkon Bashi. Kana a baya bayan nan ma, an jiyo sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen, na cewa wai Sin ta yiwa shirin tattaunawa game da lamunin da kasar Zambia ke karba kafar ungulu.

Idan muka bibiyi wannan kalamai na Janet Yellen, za mu ga ba su da tushe ko kadan, domin kuma su kansu mahukuntan kasar Zambia sun musanta hakan, suna masu bayyana kalaman da cewa sam ba su dace su fito daga bakin babbar jamiar Amurka ba. Har ma wasu masu fashin baki na cewa bai dace jamiar ta furta kalamai masu nasaba da alakar Sin da Zambia, yayin da take ziyarar aiki a Zambia ba, domin da farko ma hakan ya sabawa daar ayyukan diflomasiyya.

  • Xi Jinping Ya Gabatar Da Sakon Bidiyo Ga Taron Koli Karo Na 7 Na Kungiyar Kasashen Latin Amurka Da Caribbean

Kaza lika, matsayar Sin game da bashin dake tsakaninta da Zambia a bayyane take, kasancewar Sin da Zambia kawaye ne na tsawon lokaci, kuma abokan hadin gwiwar samar da ci gaba. Ana iya shaida hakan, idan aka dubi yadda Sin ta tallafawa Zambia da kudaden gudanar da layin dogo da ya hada Tanzania da Zambia tun a shekarun 1970, lokacin da ita kanta Sin ba ta da cikakkiyar wadata.

Har ila yau a yanzu ma, Sin ta samar da kudaden aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a Zambia, wanda hakan ke dada tabbatar da aniyarta ta ingiza ci gaban kasar.

Ko shakka babu, kalaman waccan jamia ta Amurka sun sabawa kaida, kuma akwai bukatar tsagin Amurka ya yi amfani da damarsa, ta inganta alaka da Zambia wajen gabatar da agaji na kara bunkasa kasar, maimakon mayar da Sin abun suka a idon sahihan kawayen ta na nahiyar Afirka.

LABARAI MASU NASABA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Wasu dai na kallon irin wadannan kalamai daga jamian Amurka, a matsayin kunna wutar yakin cacar baka, da nuna alamu na wata mummunar takara tsakanin ta da sauran kasashen duniya dake kawance da kasashen Afirka. Har ma wasu na cewa, idan har Amurka ba ta sauya matsa wajen kallon Sin a matsayin wata barazana ba, hakan na iya zama manuniya dake tabbatar da cewa, burin Amurka shi ne mayar da nahiyar Afirka fagen dagar takara, maimakon wuri da za a tallafawa ya samu ci gaban da yake fata, kuma nahiya da ke bukatar hadin kan dukkanin kasashen da suka ci gaba, ta yadda za a gudu tare a tsira tare! (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Daga Birnin Sin

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
Daga Birnin Sin

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Daga Birnin Sin

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Next Post
Ku Daina Bin Layin Bankuna, Ku Cire Kudi A Wajen Masu POS – CBN Ga Kwastomomi

Ku Daina Bin Layin Bankuna, Ku Cire Kudi A Wajen Masu POS - CBN Ga Kwastomomi

LABARAI MASU NASABA

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

November 1, 2025
An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

October 31, 2025
Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.