Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayar da umarnin tsare wasu sarakuna biyu masu daraja ta daya a karamar hukumar Bassa a jihar saboda gazawarsu wajen kawo karshen Kashe rayuka da barnatar da dukiyoyi a rikicin kabilanci da ya barke a Jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da aka fitar dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Mohammed Onogwu, a Lokoja.
Sarakunan da aka tsare sun hada da; Ohiegba na masarautar Mozum, HRH Khalid Bukar Ali da Aguma na masarautar Bassa da HRH William Keke.
Gwamnan kuma, ya Bukaci sa ido kan shugaban jami’an ‘yan sanda dake caji ofis na sashin Karamar Hukumar Bassa da wasu nadaddu a gwamnatin domin bankado irin rawar da suke takawa wajen tayar da tarzomar da tayi sanadiyyar salwantar rayukan wadanda ba su ji ba ba su gani ba da kuma lalata dukiyoyi a yankin.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan ya bayyana cewa tarzomar ta tashi ne sakamakon zargin kisan gilla da aka yi wa wani mai sana’ar sayar da giya mai suna Bassa Komu a yankin.
Gwamnati ta ce sabon rikicin da ya barke tsakanin kabilun da ke rikici da juna a yankin ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara da kuma barnatar dukiyoyin al’umma.