Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ziyarci Saudiyya inda gana da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, da sauran jami’ai inda suka tattauna kan rikicin ƙasarsa da Rasha.
Bayan isarsa, Zelensky ya fara ganawa da Yarima bin Salman kafin wata muhimmiyar tattaunawa da wakilan Amurka kan makomar yaƙin Ukraine.
- Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria
- Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto
A gefe guda, sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, shi ma ya isa Saudiyya, inda ake sa ran za a fara tattaunawa a yau Talata.
Daga bisani, tawagar Ukraine za ta gana da wakilan Rasha.
Duk da cewa Zelensky ba zai halarci taron na Talata ba, ya ce tawagarsa za ta ƙunshi manyan jami’an gwamnatinsa, ciki har da shugaban ma’aikatansa, ministan harkokin wajen ƙasar, da ministan tsaro.
A nata ɓangaren, Amurka ta ce za ta yi amfani da wannan dama don fahimtar matsayin Ukraine kan kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin ta da Rasha.












