Shugaba Volodymyr Zelensky na Kasar Ukraine zai gana da Joe Biden na Amurka yau Laraba a fadar White House yayin ziyarar da ya ke kai wa Washington, ganawar da za ta mayar da hankali kan tallafin da kasar za ta bai wa Kiev a yakin da ta ke da Rasha.
Ziyarar wadda aka tsara ta a asirce na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugaba Vladimir Putin na Rasha ke shirin ganawa da manyan hafsoshin sojin kasar don jin bahasi kan nasarorin kasar a yakin da ta ke da Ukraine tare da tsara muradan da suke fatan cimma a shekara mai zuwa.
- Taliban Ta Haramtawa Mata Karatu A Jami’a A AfghansitanÂ
- Abokan Hamayyata Ba Su Da Nagarta – Tinubu
Kakakin fadar White House, Karine Jean-Pierre cikin sanarwar da ta fitar game da ziyarar ta Zelensky, ta ce yayin tattaunawar Amurka za ta sake jaddadawa Ukraine cikakken goyon baya a yakin da ta ke, haka zalika za ta aike da sako ga Rasha kan hadin kan kasashen yammaci.
Ziyarar dai ita ce irinta ta farko da Zelensky ke kai wa wajen Ukraine tun bayan faro yakin kasar da Rasha a watan Fabarairu, inda ake sa ran ya gabatar da jawabi ga zaman majalisar kasar.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter Zelensky, tsohon dan wasan barkwanci da ya juye shugaban kasa, ya ce yana kan hanya don karfafa goyon bayan kasashen yammaci ga Kiev.