Ƙasar Zimbabwe ta soke hukuncin kisa bayan Shugaba Emmerson Mnangagwa ya sanya hannu kan sabuwar doka.
Sabuwar dokar ta mayar da hukuncin kisa zuwa zaman kaso na ɗaurin rai dai, kuma kimanin mutane 60 za su amfana da wannan canji a ƙasar.
- Takardun Kuɗi Sun Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 4.8 Duk Da Ƙarancin Kuɗi A Nijeriya
- Shugabannin Sin Da Rasha Sun Mikawa Juna Sakon Murnar Sabuwar Shekara
Tun shekaru da dama ake cece-kuce kan hukuncin kisa, duk da haka, kotuna suna yanke hukuncin kisa kan laifuka irin su kisan kai, cin amanar ƙasa, da ayyukan ta’addanci.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam, Amnesty International, ta yi maraba da wannan mataki, tana mai bayyana shi a matsayin abin tarihi.