• Leadership Hausa
Tuesday, May 30, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ziyarar Nancy Pelosi Zuwa Taiwan Takala Ce Mai Muguwar Manufa

by CMG Hausa
10 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Ziyarar Nancy Pelosi Zuwa Taiwan Takala Ce Mai Muguwar Manufa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A daren Talatar 2 ga watan Agustan shekaran nan ne kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Nancy Pelosi ta dira a tsibirin Taiwan na kasar Sin, duk da cewa kasar Sin ta gargadi kasar Amurka tun kafin Nancy Pelosi ta tashi daga Amurka.

Wannan halin dai irin na mai kunnen kashi da Amurka ta dauka na shirya ziyarar kakakin majalisa Pelosi dai abu ne wanda ya keta ‘yancin mulkin kasar Sin da tsokana da shiga sharo ba shanu a harkokin cikin gidan kasar.

  • Ziyarar Nancy Pelosi A Yankin Taiwan Ta Tsananta Halin Da Yankin Ke Ciki Tare Da Zubar Da Kimar Amurka A Duniya

Tun farko dai shuwagabanin kasashen biyu na Sin da Amurka wato Xi Jinping da Joe Biden sun tattauna a wayar tarho, inda shugaba Xi ya ja kunnen kasar ta Amurka da cewa duk wanda ya yi wasa da wuta to ya tabbatar da shi za ta kona.

Sanin kowa ne dai cewa kasar Sin daya ce tak a duniya kuma Taiwan yanki ne na kasar, a kan wannan, kasar Amurka ma ba ta musanta haka ba domin Sin da Amurka sun cimma yarjejeniyar kulla huldar diplomasiyya a shekarar 1978, inda Amurkar ta amince da gwamnatin jamhuriyar jama’ar Sin a matsayin halastacciyar gwamnati daya kacal na kasar ta Sin, kuma jama’ar Amurka za ta kiyaye hulda da jama’ar yankin Taiwan ta fannonin al’adu da ta kasuwanci da sauransu, amma ban da ta sassan gwamnati.

Taiwan dai tsibiri ne kuma yanki ne a karkashin jamhuriyar jama’ar Sin wanda yake kudu maso gabashin kasar.

Labarai Masu Nasaba

Kasar Sin Ta Tuntuba Tare Da Musayar Ra’ayi Da Dukkan Bangarori Game Da Warware Rikicin Ukraine A Siyasance

Sin Da Afirka Sun Fi Bukatar Kara Hadin Gwiwa Da Juna

Mutanen Taiwan dai Sinawa ne kuma yarensu da al’adunsu duka na Sinawa ne.
Haka kuma kamar yadda muka sani, Taiwan ba kasa mai zaman kanta ba ce kuma ba ta da mazauni a majalisar dinkin duniya MDD ko a kungiyoyin kasa da kasa irin na gwamnati, don haka ma ne, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya nuna rashin jin dadinsa da ziyarar Pelosi wadda take neman ta da zaune tsaye da kawo rudani a zaman lafiya a yankin gabashin Asiya da ma duniya baki daya.

Babban sakatare Guterres ya yi bayani cewa za a tsaya tsayin daka kan kudurin kasancewar kasar Sin daya ce tak a duniya.

Kasashe dai fiye da 160 ma suka yi tir da ziyarar Pelosi da nuna goyon bayansu ga kasar Sin da kuma bayyana cewa ziyarar ta keta dokokin kasa da kasa da manufar nan ta kasar Sin daya ce tak a duniya kuma Taiwan yanki ne na kasar Sin.

Wannan ziyara dai a ganina na mai lura da harkokin kasashen waje, babban kuskure ne kasar Amurka ta tafka, kuma takala ce da yin katsalandan a harkokin cikin gida na kasar Sin. Haka zalika, abin lura ne Amurka na yin amfani da gurbatacciyar siyasa a yankin Asiya domin wata manufarta. A sakamakon sa ido da katutu da Amurka ke yi a yankin ya sa kasashe da dama suna yin tir da halayenta na neman fitina.

Hakazalika ban da ta da zaune tsaye da tsokana da wata manufa ban ga amfanin da ziyarar Pelosi za ta kawo wa yankin Taiwan ba da kawo halin zaman doya da man ja a huldar da ke tsakanin kasar Sin da Amurka.

A yanzu haka dai wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin kasar Sin da Amurka a yayin da kasar Sin ta yi martani ta hanyar dakatar da wasu yarjejeniyoyi da ake yi tsakanin kasashen biyu a baya. Ita ma Nancy Pelosi ta samu nata a yayin da kasar Sin ta kakaba mata tare da iyalanta takunkumai da suka dace da tanadin dokokin jamhuriyar jama’ar kasar Sin.

Wannan dai duk abubuwa ne wadanda ya kamata kasar Amurka ta san cewa kasar Sin ba za ta zauna ta yi shiru ba idan aka ci zarafinta ba.

Ya kamata kuma Amurka ta lura cewa Allah wadai da kasashe suka yi a kan wannan ziyara wani abu ne da zai rage mata girmamawa a idon duniya baki daya saboda abin da zai haifar sakamakon ziyarar zai iya shafar kasashen duniya da ba su san hawa ba bare sauka ba. (Lawal Sale)

ShareTweetSendShare
Previous Post

An Saki Tsofaffin Gwamnoni, Dariye Da Nyame Daga Gidan Yarin Kuje

Next Post

“El-Rufai Zai Koma PDP Kafin 2023”

Related

Kasar Sin Ta Tuntuba Tare Da Musayar Ra’ayi Da Dukkan Bangarori Game Da Warware Rikicin Ukraine A Siyasance
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Tuntuba Tare Da Musayar Ra’ayi Da Dukkan Bangarori Game Da Warware Rikicin Ukraine A Siyasance

7 hours ago
Sin Da Afirka Sun Fi Bukatar Kara Hadin Gwiwa Da Juna
Daga Birnin Sin

Sin Da Afirka Sun Fi Bukatar Kara Hadin Gwiwa Da Juna

8 hours ago
An Wallafa Littafi Kan Jawabin Shugaba Xi Jinping A Wajen Taron Kolin Kasar Sin Da Yankin Tsakiyar Asiya
Daga Birnin Sin

An Wallafa Littafi Kan Jawabin Shugaba Xi Jinping A Wajen Taron Kolin Kasar Sin Da Yankin Tsakiyar Asiya

9 hours ago
Za A Harba Kumbon Shenzhou-16 A Gobe Talata
Daga Birnin Sin

Za A Harba Kumbon Shenzhou-16 A Gobe Talata

10 hours ago
Ya Dace Amurka Ta Koyi Hikimomin Kissinger Don Yin Mu’amala Da Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Ya Dace Amurka Ta Koyi Hikimomin Kissinger Don Yin Mu’amala Da Kasar Sin

11 hours ago
An Kammala Bikin Baje Kolin Fasahohin Tattara Manyan Bayanai Na Kasa Da Kasa Na Sin
Daga Birnin Sin

An Kammala Bikin Baje Kolin Fasahohin Tattara Manyan Bayanai Na Kasa Da Kasa Na Sin

13 hours ago
Next Post
“El-Rufai Zai Koma PDP Kafin 2023”

"El-Rufai Zai Koma PDP Kafin 2023"

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Tuntuba Tare Da Musayar Ra’ayi Da Dukkan Bangarori Game Da Warware Rikicin Ukraine A Siyasance

Kasar Sin Ta Tuntuba Tare Da Musayar Ra’ayi Da Dukkan Bangarori Game Da Warware Rikicin Ukraine A Siyasance

May 29, 2023
Sin Da Afirka Sun Fi Bukatar Kara Hadin Gwiwa Da Juna

Sin Da Afirka Sun Fi Bukatar Kara Hadin Gwiwa Da Juna

May 29, 2023
Tinubu Ya Taya Erdoğan Murnar Nasarar Cin Zaben Shugaban Kasar Turkiyya

Tinubu Ya Taya Erdoğan Murnar Nasarar Cin Zaben Shugaban Kasar Turkiyya

May 29, 2023
Sabon Gwamnan Sakkwato Ahmed Aliyu Ya Nemi Goyon Bayan ‘Yan Adawa A Jihar

Sabon Gwamnan Sakkwato Ahmed Aliyu Ya Nemi Goyon Bayan ‘Yan Adawa A Jihar

May 29, 2023
An Wallafa Littafi Kan Jawabin Shugaba Xi Jinping A Wajen Taron Kolin Kasar Sin Da Yankin Tsakiyar Asiya

An Wallafa Littafi Kan Jawabin Shugaba Xi Jinping A Wajen Taron Kolin Kasar Sin Da Yankin Tsakiyar Asiya

May 29, 2023
Mamallakin Tashar Talebijin Ta AIT, Raymond Dokpesi Ya Rasu A Abuja

Mamallakin Tashar Talebijin Ta AIT, Raymond Dokpesi Ya Rasu A Abuja

May 29, 2023
Za A Harba Kumbon Shenzhou-16 A Gobe Talata

Za A Harba Kumbon Shenzhou-16 A Gobe Talata

May 29, 2023
Ya Dace Amurka Ta Koyi Hikimomin Kissinger Don Yin Mu’amala Da Kasar Sin

Ya Dace Amurka Ta Koyi Hikimomin Kissinger Don Yin Mu’amala Da Kasar Sin

May 29, 2023
An Kammala Bikin Baje Kolin Fasahohin Tattara Manyan Bayanai Na Kasa Da Kasa Na Sin

An Kammala Bikin Baje Kolin Fasahohin Tattara Manyan Bayanai Na Kasa Da Kasa Na Sin

May 29, 2023
Jagoranci Za Mu Yi Ba Mulkin ‘Yan Nijeriya Ba – Tinubu

Abubuwa 5 Da Gwamnatin Tinubu Za Ta Mayar Da Hankali Kan Su

May 29, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.