A karshen wannan mako da ya gabata ne, LEADERSHIP Hausa ta yi tattaki zuwa kauyen Degel da ke karkashin Gundumar Chimmola, a Karamar Hukumar Gwadabawa ta Jihar Sokoto.
Kauyen Degel yana da kimanin tazarar kilomita 60 daga birnin Sokoto ta bangaren Arewa Maso Gabas, kuma gari ne mai dimbin tarihi, wanda ba a Nijeriya kadai ba, shahararre ne ga Malaman tarihi da masana a Afirka ta Yamma.
Degel ya shahara ne sakamakon kasancewarsa garin da aka haifi Shehu Usman Danfodiyo, sannan kuma a nan ne ya gudanar da rayuwarsa ta neman ilimi, koyar da ilmai daban-daban tare da kaninsa, Mallam Abdullahi Gwandu, da dansa Amiril Muminin, Muhammadu Bello da sauran hazikan almajiransa wadanda suka taimaka masa wajen aikin yada ilimin addinin Musulunci, kiran jama’a zuwa ga kyautata shi, kana da dora tubalin jihadin da ya jagoranta na kafa Daular Islama, wurin shekarar 1774 zuwa 1804, yayin da garin Degel ya girmi birnin Sokoto da shekaru masu yawa.
Bugu da kari, a tattaunawar mu da wani dattijo, mai kula da Hubbaren Degel, Baba Ahmadu Mai Hubbare, ya ce duk da yanzu garin kufayi ne (babu kowa), ya bayyana cewa cike yake da kaburburan bayin Allah masu yawa, wadanda suka kunshi; Kabarin Shehu Muhammadu Fodiyo (Mahaifin Shehu Usmanu Danfodiyo), kabarin matar Shehu Usmanu, kuma mahaifiyar Nana Asma’u, Sayyida Muna, kabarin Imam Muhammad, da kuma na Shehu Zangi, Muhammadu Jabbo, Hauwa’u Matar Muhammad Fodiyo, tagwayen Shehu Usmanu, Sidi Halidu dan Shehu Usmanu, Sidi Ummaru dan Shehu Usmanu, da makamantan su.
Bugu da kari, Baba Ahmadu ya ci gaba da zagayawa da ni ya na nuna mini wurare daban-daban na gargajiyar gidan, ciki har da shacin inda gidan Shehu Mujaddadi yake tare da nuna wani bangare wanda ya ce a nan ne Shehu Mujaddadi yake zama kuma nan ne kamar cibiyar da yake koyar da ilimai daban-daban, wanda masana tarihi suke kiransa da Jami’ar Shehu Usmanu Mujaddadi.
Wannan waje ne wanda sai dai kwatamce ko wasu alamu dake nuna jama’a sun yi rayuwa a wajen; akwai itatuwan goriba a ciki, mainoni (dogon-yaro ko darbejiya) da aduwa tare da sauran itatuwan gida. Haka kuma, dadewa ta sanya babu zahirin wasu kaburbura face alamu, wasu kuma an zagaye su da duwatsu.
Yayin da masu kula da Hubbaren suka bayyana cewa akwai gidajen wasu dake makobtaka da Shehu Usmanu Mujaddadi, wanda suka hada da:
Ta bangaren gabas, akwai gidan Mallam Muhammad Kwairanga, Mallam Ummaru Dumama, Mallam Muha (Mallami ne daga kasar Azbin), Shehu Abdullahi Gwandu (kanin Shehu), Shehu Musdafa.
A bangaren yamma daga gidan Shehu akwai gidan Mallam Aliyu, yaya ne ga Shehu, sai Mallam Musdafa, wanda yake matsayin Sakataren Shehu, Sheikh Muhammad Sambo; Kudu daga gidan Shehu akwai gidan Mallam Ummaru Alkammu, aboki na kut-da-kut ga Shehu, sai Mallam Kawmanga, da ne ga ‘yar uwar Shehu, Mallam Sulaiman Wodi dan aiken Shehu zuwa ga Sarkin Gobir.
Wadannan gwarazan bayin Allah, su ne wadanda suka sadaukar da rayuwarsu, lokacin su da dukkan abin da suka mallaka wajen taimaka wa Shehu Mujaddadi wajen tsamar da al’umma daga duhun jahilcin cudanya kirkirarru kuma fandararrun al’adun da suka ci karo da koyarwar Musulunci wadanda gurbatattun mallamai suka jingina zuwa ga addinin Musulunci a matsayin hanyar rayuwa.
Haka kuma, sun fuskanci kowace irin barazana da kalubale wajen wanzar da addinin Musulunci a wannan nahiya.
Masana sun yi cikakken bayani dangane da ingantattun sauye-sauyen da wannan jihadi na Shehu Mujaddadi ya jagoranta, mai cibiya a kasar Hausa Sokoto, gwagwarmayar da suka ambata a matsayin wadda ta samar wa da Yammacin Afrika kima da martaba a tsakanin sauran nahiyoyi, sannan ‘yanci ne wanda ya taimaka wa kasashen yankunan Masina da Tukolor samun kumaji da karsashin kafa Dauloli a bangarensu.
Haka zalika, jihadin Mujaddadi Shehu Usmanu ya kafa ginshiki a fannin sauyin rayuwa, gudanarwar da sha’anin mulkin al’umma da tsara ci gaban tattalin arziki a wannan nahiya da ma sauran yankunan kasashen Afrika.
Sauyin da ya haifar da Daular Musulunci, mai cibiya a Sokoto, raya ilimin addinin Musulunci a zukatan al’umma, sannan da shimfida sabon shafi a fannin bunkasa ilimi.
Ko shakka babu, wannan yunkuri da Shehu Mujaddadi ya yi tare da goyon bayan almajiransa da sauran al’ummar Musulmi, ya taimaka gaya wajen dawo da martabar Nijeriya da ma Yammacin Afrika baki daya.
Wani muhimmin abu da jihadin ya kawo shi ne rayawa da bunkasa fannin, saboda babu abu mafi muhimmanci da ya wuce ilimi wajen kawo sauyi mai ma’ana a ci gaban al’umma, tare da bayar da gagarumar gudumawa wajen wanzuwar addinin Musulunci.
Baya ga wannan, wayar da kan al’umma zuwa ga koyarwar Addinin Musulunci na gaskiya, Shehu Mujaddadi, dan uwansa, Mallam Abdullahi Gwandu, dansa Muhammadu Bello tare da sauran almajiransa, sun dukufa wajen aikin wallafa daruruwan littafai a fannoni ddaban-daban na ilimi, domin al’ummar duniya ta ci gaba da morar ayyukan da suka yi na hidimta wa Addinin Musulunci.
Tun bayan umurnin da Sarkin Gobir Yumfa Bawa Jan-Gwarzo, cewa Shehu tare da mabiyansa su bar kasarsa, inda hakan ya sanya suka koma wani waje, wanda ke iyaka tsakanin Gobir da Kebbi da ake kira Gudu.
Kana daga baya Sarkin Gobir ya ayyana yakar Shehu da da’awarsa; inda hakan ya tilasta musu kare kansu, al’amarin da daga bisani suka samu nasara da galaba kan Sarakunan Habe (Hausawa), da kafa Daular Musulunci a birnin Sokoto.
Sakamakon kalubale da yawaitar hare-haren da wannan Daula mai cibiya a Sokoto ke fuskanta, hakan ya jawo dole aka samar da sansanonin dakile farmakin makiya a kowace kusurwar birnin Sokoto; Gabas aka ajiye sansani a Wurno, Arewa Maso Gabas aka kafa sansanoni a Chimmola da Gwadabawa, domin dakile Gobirawa, Kabawa da Azbinawa, sai bangaren Yamma aka samar da na Gwandu da makamantansu.
Wannan su ne dalilan da suka hana garin Degel ya samu cikakkiyar kulawar da ya dace a wancan lokacin, wanda sai daga baya Sarakunan Musulmi da Gwadabawa suka dauki matakin kula da shi a matsayinsa na tushe.
Har ila yau, tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu; duk da garin a daji yake, amma bai hana daruruwan maziyarta zuwa wajen ba, kama daga wasu bangarori jamhuriyar Nijar, Kamauru da Chadi, wasu kuma daga jihohin Adamawa, Bauchi, Gombe da Taraba da sauransu.
Ya dace a ce gwamnatin Tarayya da ta Jihar Sokoto su sake duba yiwuwar daukar kwararan matakan inganta wannan muhimmin waje, sakamakon dimbin tarihi da tasirin da yake da shi.
Ko ba komai garin Degel cibiya ce ga duk wani nau’in ci gaban da Nijeriya take da shi a fannonin rayuwa daban-daban. Sannan ta fannin Addinin Musulunci da ci gaban kyawawan al’adun al’ummar Musulmi, waje ne mai matukar tasiri wanda bai dace a ce ya ci gaba da kasancewa irin yadda yake yanzu ba.
Wannan Hubbare ce wadda ta kunshi kaburburan dimbin bayin Allah, kama daga shi mahaifin Shehu Usmanu Mujaddadi, zuwa sauran waliyan da suke tare da shi, wanda mu kaddara Shehu Usmanu yana da rai, muna ganin zai kyale wajen ya ci gaba da kasancewa a halin da yake ciki yanzu?
Wanda halin da ake ciki akwai bangarorin Hubbaren da mutum ba zai iya shiga ba, saboda yadda suka koma surkukin dajin da ya tattaro macizai da sauran kwari masu lahani, sannan babu dakunan saukar baki, babu ruwan sha, babu hasken wutar lantarki, babu masallaci ballantana dakin ajiye littafai da kayan tarihi a wajen, sannan uwa uba ba a kula da wani dattijon da na tarar a matsayin mai aikin shara da kula kaburbura a Hubbaren.
Sakamakon rashin kulawar gwamnatin Jihar Sokoto yadda ya kamata da masarautun da Daular Usmaniyya ta kafa kamar wajen rage kima da tasirin wannan Hubbaren, wanda sam bai dace a ce an bar wannan waje mai daraja ya tozarta ba.
Sannan duk da wadannan tarin matsalolin da Hubbaren ke fuskanta, bai hana dubun dubatar al’ummar wasu nahiyoyi, kasashe da jihohin kasar nan zuwa ziyara ba. Masu hikimar magana sun ce: Tuwon Girma miyarsa nama.
Kamar sauran kasashe da al’ummar da suka ci gaba wajen kiyaye wuraren tarihi yana da matukar muhimmanci tare da alfanun taskace abubuwan da magabata suka yi wajen sadaukarwa da muhimman ayyukan da suka gudanar domin a kalla a rika tuna su tare da kwaikwaya, saboda ko shakka babu, Shehu Usmanu Mujaddadi tare da kaninsa da almajiransa sun bayar da gagarumar gudumawa wajen wanzuwar Addinin Musulunci, al’adu da martabar wannan al’ummar, kuma bisa ga hakikanin gaskiya al’ummar Nijeriya suna da bukatar hakan.
Kuma wadannan bayin Allah sun cancanci mu girmama su, mu wanzar da ambaton su tare da yi musu hidima tamkar yadda suka yi wa Addinin Musulunci da al’umma hidima.
A ma’aunin adalci, Shehu Usmanu Mujaddadi yana bin duk Musulmin Nijeriya bashi. Saboda haka wajibi ne raya duk wani abin da suka samar, saboda turbar da suka tafi a kai ita ce hanya ta gaskiya wadda ta dace da rayuwarmu ta addini, dabi’a da al’ada.