Bisa al’ada, a farkon kowacce sabuwar shekara, ministan harkokin wajen kasar Sin kan ziyarci wasu kasashe a nahiyar Afrika. Kuma a bana ma hakan ce ta kasance, inda sabon ministan harkokin wajen Sin Qin Gang, ya fara ziyararsa a kasashen Afrika daga jiya Litinin, wadda kuma ita ce ziyararsa ta farko a ketare bayan dare kujerar.
Dangantakar kasar Sin da Afrika ba sabon abu ba ne, la’akari da cewa, wannan al’ada ta ziyarar ministan harkokin wajen Sin a nahiyar Afrika a duk farkon shekara, ta shafe shekaru 33 a jere ana gudanar da ita ba fashi. Wannan ya tabbatar da kasar Sin a matsayin jajirtacciya, mai cika alkwarinta, duk wuya duk rintsi. Haka zalika, ya nuna yadda Sin take daukar kasashen Afrika da muhimmanci, sabanin wasu kasashen dake daukar nahiyar a matsayin wurin yi wa babakere ko ci da gumin al’umma ko kuma neman cikar wasu burikansu na siyasa.
Ba shakka, karfin alakar kasar Sin da Afrika ta zarce tunanin mutum, shi ya sa ma masu yada jita-jita da neman danniya da adawa da Sin, ke neman shafa mata bakin fenti domin shiga tsakaninta da kasashen Afrika. Sai dai, abun da ya kamata a fahimta shi ne, da kasar Sin tana da wata mummunar manufa dangane da alakarta da kasashen nahiyar da an gani a fili zuwa yanzu, kamar yadda aka ga dimbin ayyukan more rayuwa da ta yi, kuma take ci gaba da yi a kasashen.
Albarkacin kasar Sin, kasashen Afrika sun samu ci gaban tattalin arziki da zaman takewa da ingantuwar tsaro da fasahohi da kwarewa da kuma muhimman ababen more rayuwa da ba su samu ba daga iyayen gidansu masu mulkin mallaka.
Har ila yau, a wannan lokaci da ziyarar na ministan Sin din ya zo a daidai lokacin da kasar take saukaka matakanta na yaki da annobar COVID-19 da na shige da fice har ma da kyautata bangarorin zuba jarin waje, wata dama ce ga kasashen nahiyar na farfado da harkokinsu na kasuwanci da kasar Sin da fadada hadin gwiwa a bangarori daban-daban, domin wannan dama ce ’yan kasuwar Afrika suka dade suna jira, wanda zai taimaka wajen karfafa tattalin arzikinsu da rage tashin farashin kayayyaki da suke fama da shi.