Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da daukaka darajar kwalejin Mustapha Umar Elkanemi ta karatun Larabci da ke Maiduguri zuwa wata babbar cibiya ta musamman ta koyar da ilimin larabci da ilimin addinin Musulunci domin yaki da irin fahimtar da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi wa Karatun Addinin Musulunci.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin da ya kai ziyarar duba kwalejin domin shirye-shiryen sauya tsarin kwalejin.
- ISWAP Ta Hallaka Kwamandan Boko Haram A Sambisa
- Cire Tallafin Fetur: Zulum Ya Kaddamar Da Motoci 70 Don Saukaka Zirga-zirgar Al’umma.
Wannan tsarin dai, an yi shi ne da nufin dakile irin fahimtar da kungiyar Boko Haram ta yi wa addinin Musulunci. Kungiyar ta yi kaurin suna wajen tsaurin ra’ayi da ikirarin da’awar addinin Musulunci da kafa gwamnatin musulunci sabida sabanin fahimtar karantarwar addinin.
“Idan aka kafa sabuwar cibiyar, za ta kasance karkashin karantarwar Jami’ar Al-Azhar da ke birnin Alkahira ta Misra kuma za ta dinga ya ye daliban da za a tura su kananan hukumomin Borno 27 domin yin wa’azin da zai dakile akidar Boko Haram.”
Don haka, Gwamna Zulum ya umurci sabuwar hukumar ilimin Larabci da Tsangaya da aka kafa ta jihar Borno da ta karbi ragamar tafiyar da dukkanin makarantun Tsangaya da na islamiyya a jihar Borno.