Matashiyar marubuciya da tauraronta ke haskawa a duniyar marubutan yanar gizo, Minab ‘Yar Baba ta bayyana jin dadi da farin cikinta yadda marubutan suke mu’amalantar juna tamkar ‘yan uwan da suke ahali daya ba tare da nuna bambanci tsakaninsu ba.
Wanda a cewarta hakan wani sirri ne daga sirrikan bunkasar rubutu da marubutan Hausa a fadin duniya. Ga dai yadda tattaunawarta ta kasance tare da wakilinmu, Adamu Yusuf Indabo:
Wace ce Manab ‘Yar Baba?
To da farko dai cikakken sunana shi ne Maryam Nasir Ibrahim, wadda a duniyar rubutu aka fi sanina da Manab ‘Yar Baba. An haife ni a garin Kano ce, na yi karatuna na bangaren addini da boko duka a nan birnin Kano.
To ta ya kika tsinci kanki a duniyar rubutu?
Rubutu wani abu ne da na taso da shaukinsa, tun a lokacin ban fahimci me ake nufi da rubutu ba ko nake jagwalgwalona da sunan rubutu. Na fara rubutu tun ina JS 1 a edercise book, zan zauna na rubuta, na kuma tara classmates ina karanta musu, ko kuma na ba su labari ba tare da na rubuta ba. Daga baya na fara rubutu a online a lokacin da ban zata ko shiryawa hakan ba. Shigata duniyar rubutu ya samo asali ne da karfin gwiwa da na samu, wanda har yanzu ba zan iya mantawa da hakan ba.
Yaushe kika fara rubutu, zuwa yanzu kin rubuta littafai nawa?
Na fara rubutu a ranar wata Talata da ta yi daidai Shida ga watan Takwas a shekarar Dubu Biyu Da Shatara (06/08/2019). Littafina na farko da na rubuta shi ne MONAH. Amma yanzu haka na rubuta littafai guda Bakwai (7) su ne:Monah, Iya Ruwa, Kanin Ajali, Jannat, Madafa, Laifin Waye? Da kuma Sai Na Dauki Fansa. Amma shi sai na dauki fansa na hadin gwiwa ne.
To cikin wadannan littafai guda 7 wanne bakandamiyarki?
JANNAT shi ne bakandamiyata. Saboda cikinsa akwai babban lamari da ya bambanta shi da sauran littafaina. Labarin Jannat labari ne da na gina sa a kan nuni da wasu halayya da suke da matsala a rayuwa, kamar munafurci, hassada da kyashi, karya da dai sauransu. Amma jigon labarin shi ne nuni da nusar da illar son kai, a ta wani bangaren kuma soyayya. Kuma da yawan labarin abubuwa ne da suka faru a gaskiyance. Shi ya sa lokacin da nake rubutunsa na jingine komai na tattara hankalina gare sa. Kuma Alhamdulillah! Ya samu karbuwan da ban yi tunanin haka ba.
To cikin littafan kuma wanne ya fi ba ki wahala wajen rubutunsa?
MADAFA ya fi ba ni wahala, dan na ma a jesa a gefe guda, har yau na kasa kammala sa. Wani lokaci nakan dauko shi kamar zan ci gaba amma sai lamarin ya citira. Saboda al’adun mutanen ciki, da ratuwarsu. Domin magana ce da ake ta shudaddan lokaci, karni Uku da ya wuce. Shi ya sa yake da wahala, dole sai da bincike a kai, domin komai na lokacin da ne, wanda yake daban da na yanzu.
Cikin wanne irin yanayi kika fi jin dadin yin rubutu?
A yanayi na kadaici, na fi jin dadin yin rubutu a lokacin.
Daga fara rubutunki zuwa yau, wanne nasarori kika cimma ta sanadin rubutu?
Alhamdulillah! Daidai gwargwado na samu nasarori sanadiyar rubutu, ko bangaren ilimi ma na san nasara ce, dan akwai abubuwa da yawan da sanadin rubutu na san su.
Ya batun kalubale?
Kalubale! Tam ita rayuwa dama ta gaji haka, idan kana abu ba ka samu kalubale ba a kansa kai karan kanka sai ka tsargu, sai dai kuma in ka ce za ka mayar da hankali a kan haka, to ba za ka taba gaba ba, dan kwan gaba kwan baya mutum zai ta yi. Alhamdulillah ni kalubalen da na fuskanta sun zame min alkhairi a gare ni, domin ana daukar darasi ne daga kuskure.
Wanne sako kike da shi ga masoyanki?
Sakona ga masoya a ina matukar godiya da kaunarku a gare ni, ku ne karfin gwiwata, ina yi muku fatan alkhairi a rayuwarku.
‘Yan uwanki marubuta, wanne kira za ki yi gare su?
Marubuta! Bayin Allah! Hakika kuna himdimtawa al’umma ta hanyar ilimantar da su tare da nishadantarwa da kuma fadakarwa, Allah ya yi mana jagora. Sai dai ina kira da baragurbin marubuta da dan Allah su dakata haka nan, su tsaftace al’kalumansu da tunaninsu, domin rubutu tunanin marubuci ne. Sannan mu tuna abu biyu, na farko sau tari makaranci ya na daukar tunanin marubuci, ya ce zai yi amfani da shi a duniyarmu ta zahiri, ka ga ke nan rubutu yana zama silar gyara da kuma bata tarbiya, in rubutunki/ka ya zama silar gyara to kina/kana da lada, in kuma akasin haka ne shi ma haka ne. Na biyu a duk lokacin da muka rubuta kalma daya mu tuna da sai fa an tambaye mu a ranar da bakinmu ba zai magana ba. Sannan sai dan wani abu da nake son magana a kansa, dan Allah kafin mu rubuta mu san mene ne ake nufi da rubutu? Ya ake yin rubutun nan? Mene ne ka’idojin rubutu? Da dai sauransu.
A karshe ina mika sakon girmamawa da gaisuwa ga manyan da kananan marubuta, da fatan Allah ya yi mana jagora ya kiyaye mana alkalumanmu ga janyo mu ga halaka. Kuma ya bar mana zumuncinmu, domin zumunci da hadin kan marubuta na matukar burge ni.
Hajiya Manab ‘Yar Baba muna godiya.
Ni ma na gode sosai da wannan damar.