'Yan Bindiga Sun Tarwatsa Gadar Ngala A Borno

Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun tarwatsa wata babbar gada da ke Ngala a jihar Borno mai makwabtaka da kasar Kamaru.

Hakan ya haddasa katse daya daga cikin muhimman hanyoyin sufuri tsakanin Nijeriyar da kasar Kamaru abinda zai iya janyo tsaiko wajen kai wa mutane kayayyakin agaji.

Mazauna yankin sun ce akwai tarin kananan da manyan motoci dauke da kayan masarufi wadanda suka kasa tsallakawa ta gadar Ngala din.

Watakila An Harbo Jirgin Malaysia Bisa Kuskure, Cewar Jami’an Tsaro

Manyan jami'an leken asirin Amurka sun ce bayani da watakila za'a yi akan jirgin saman Malaysia da ya fadi a gabashin Ukraine shi ne 'yan aware da ke goyon Rasha sun harbo jirgin ne bisa kuskure.

Jamian leken asirin da aka sakaya sunayensu sun ce yayinda Rasha ke samarwa 'yan tawaye da makamai, amma Amurka ba ta da kwakwarar hujja akan makamin da aka yi amfani da shi wajen harbo jirgin saman,Rasha ce ta samar da shi.

Jihar Kano Zata Bi Sahun Manyan Biranen Duniya

Za'a kawata sufiri a birnin Kano

Jihar Kano zata bi sahun manyan biranen duniya wajen samar da sufiri na zamani. Don kuwa gwamnatin jihar ta sa hannu a wata takardar yarjejeniya ta samar da layin jirgin kasa  mai aiki da wutar lantarki da zai yi jigila a cikin birnin Kano.

Sojojin Nijeriya Sun Arce Saboda Boko Haram

Babban hafsan dakarun sojin kasan Nijeriya Laftanar Janar Keneth Minimah ya bayyana cewar wasu sojoji sun arce daga bakin aikin su saboda tsoron Boko Haram.

A cewar Minimah lamarin abin Allawadai ne kuma ya nuna cewar mutanen ba su dace da shiga aikin soja ba.

Ya kara da cewar sojan asali ba zai guje wa yaki ba, saboda an dauke shi aiki ne domin ya kare martabar kasarsa kuma ya je fagen daga.

Pages

Makaloli

Yusuf M. D. Bakura dan siyasa ne a jam’iyyar PDP ta jihar Sakkwato, kuma na hannun daman Tsohon ministan harkokin matasa, Alhaji Yusuf Suleiman, wanda ke takarar gwamna a shekarar 2015.

Daga Mustapha Ibrahim Tela da Abdullahi Mohd Sheka.