KASASHEN WAJE: Jamus Ta Zargi Trump Da Haddasa Rikicin Larabawa

0
58

Kasar Jamus ta zargi shugaban Amurka Donald Trump da kitsa rikici tsakanin kasashen Larabawa domin ganin an samu cinikin makamai.

Ministan Harkokin Wajen Jamus Sigmar Gabriel ya ce, kwangilar makaman da Saudiya ta bawa Amurka na daga cikin dalilan da suka haifar da rikicin da aka samu tsakanin Saudiyar da kawayenta musamman kasar Katar

Gabriel ya ce, ya na fargabar abin da zai biyo baya sakamakon wannan matsalar da aka samu a fadin yankin kasashen Larabawa baki daya.

A farkon makon ne kasashen Saudiya da Masar da Yemen da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrai suka katse hulda da Katar tare da rufe kan iyakokinsu na sama da na ruwa da na kasa da Katar.

Daukan wannan mataki na zuwa bayan sun zargi Katar da tallafa wa kungiyoyin ‘yan ta’adda, duk da cewar Katar din ta musanta zargin.

Shugaba Donald Trump ya ce, ziyarar da ya kai Saudiya ce ta haifar da matakin da aka dauka kan kasar Katar.

A wani labarin kuma, Sarkin kasar Kuweiti Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah ya isa birnin Riyad na Saudiyya, domin shiga tsakani da nufin shawo kan rikicin diflomasiyyar da ya barke tsakanin wasu kasashen Larabawa da kuma Katar.

Rikicin da ya sanya kasashen da suka hada da Hadaddiyar daular Larabawa, Masar, Baharain, Libya, Yemen, Maldibes a karkashin jagorancin Saudiyya suka yanke alaka tsakaninsu da kasar ta Katar.

Daga cikin matakan da suka dauka dai akwai dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tsakaninsu da ita, sai kuma rufe iyakar da ke tsakanin Katar din da Saudiyya.

Tuni dai ministan harkokin wajen kasar Katar Mohamed Bin Abdul Rahman, ya ce kasar a shirye take, ta shiga tattaunawar sulhu da sauran kasashen domin warware sabanin da ke tsakaninsu, inda ya ce Katar ba ta da niyyar daukar wani mataki na ramuwar gayya akansu domin zai shafi rayuwar al’ummomin kasashen da ke cikin kungiyar hulda da juna a yankin Gulf baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here