Shugaba Buhari Bai Karya Dokar Kasa Ba, Cewar Majalisar Dattawa

151

Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da cewa zaman Shugaba Buhari a birnin Landan  na fiye da kwanaki 90 bai saba dokar kasa ba kamar yadda ake yadawa.

A dai cikin makon nan ne wasu kungiyoyin al’umma suka gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja inda su ke kira ga shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ko dai ya koma aiki ko kuma ya sauka.

A wata sanawar da shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar dattawa, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce Buhari ya mutunta tanadin tsarin mulkin shekarar 1999 wanda ya neme shi da ya mika ragamar mulki ga Mataimakinsa tare d sanar da majalisar tarayya, kamar yadda ya aiwatar.

Sanata Abdullahi ya bukaci masu zanga zangar neman Shugab Buhari ya yi murabus kan su dakatar da yin hakan, saboda majalisar tarayya ta gamsu da irin jagorancin Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here