Tafa: A Nijeriya Ne Kaɗai A Ke Haka!

491

An shafe shekaru masu yawan gaske a na ƙiyasta cewa, watarana sai wata mummunar annoba ta afku a garin Tafa na yankin jihar Kaduna, sakamakon ajiye manyan motoci da direbobi ke yi a kan babban titin da ke kan hanyar babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja.

Kusan duk wanda ya zo wucewa ta kan wannan hanya sai ya yi maganar yadda wajen ya zama; idan bai furta a bakinsa ba, to zai yi maganar a cikin ransa. An sha samun hatsarin mota a gurin, saboda yadda manyan motocin da ke ajiyewa a gefe su ke matse hanyar ta zama ƙanƙanuwa tamkar hanyar ƙauye.

Idan ka zo wajen a mota za ka wuce ba ka yi tsaki ba, to wataƙila barci ka ke yi, saboda jinkirin wucewa da a ke samu ko kuma sakamakon gosulo da a ke yi a wajen, idan ta kama.

A wasu lokutan a kan buga rahoto a jarida ko a gidajen rediyo ko bayyana ra’ayi kan buƙatar da a ke da ita wajen ganin an ɗauki matakin da ya kamata na gina wa waɗannan direbobin manyan motoci garejin da za su riƙa ajiye motocinsu ko kuma a haramta mu su tsayawa a gefen hanyar bakiɗaya.

Har ma a kan nusar da gwamnati cewa, wannan wata dama ce da za ta riƙa samun kuɗin shiga, domin za a iya yin amfani da wannan dama a na amsar haraji a hannun duk wanda zai shiga cikin garejin. Bugu da ƙari, gwamnati za ta iya gina shaguna a ciki da wajen tashar ko garejin, wanda hakan ita wata dama ce ta samun kuɗin shiga ga gwamnati.

To, amma duk da shekarun da a ka kwashe a na yin waɗannan kiraye-kiraye, hakan bai sa gwamnatin jihar Kaduna ko gwamnatin tarayya sun farga ba.

Eh, za a iya cewa, an fara gina garejin da a ke ta faman maganarsa, to amma shekarun da a ka ɗauka a na yin aikin ba tare da an gama ba, a fili ya nuna cewa ba da gaske a yi ba.

Tabbas idan ba a irin ƙasashenmu ba, babu yadda za a yi a bar abinda a ka san zai iya ɗaukar rayukan al’umma ya cigaba da kasancewa ba tare da na ɗauki mataki a kai ba; a jira har sai annobar ta afku, sannan ne za ka ga kowane babba ko mai mulki ya na tsoma baki ko kuma fargar jaji!

Allah Ya shiryi masu ikonmu!!!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here