Yadda Zaka Kauce Wa Dogon Layi A ATM

171
PIC.1.CUSTOMERS QUEUE AT A BANK ON YAKUBU GOWON WAY, KADUNA, DURING THE TIME OF 24 HOUR CURFEW RELAXATION ON TUESDAY (26/6/12).

Daga Bakir Muhammad

Dogayen layuka na masu harkokin kasuwanci daban daban wani babban alama ne da yake nuna lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabowar shekara ya yi, hatta na’urorin ATM na cire kudi wadanda bankuna ke sanyawa basu tsira ba a irin wannan lokacin, a yayinda zaka ga dimbin jama’a na layi domin su samu damar cire kudi,

Kai ko ma ba a lokacin wadannan bukukuwan ba, an saba da mugun cunkuso da dogayen layuka a cikin bankunan Nijeriya.

Yawan masu kokarin cire kudi a ATM, yana matukar takura masu cirar kudin, sannan yana gajiyar da na’urar ATM din ita kanta, sannan guraren da suke da ATM sun zamo wani dandali na ‘yan kwace da masu sane.

Akwai wasu ‘yan shawarwari da in aka bi za a iya kaucewa wadannan matsaloli musamman a wannan lokacin da bukukuwan kirsimeti da sabowar shekara suka gabato.

Zai yi sauki ga mutum ya cire adadin kudin da zai yi amfani da shi lokacin hutun, misali sati daya, maimakon kullum ya dinga zuwa cirar kudi.

Akwai shagunan cinikayya na intanet za su taimaka wa mutum matuka wajen yin siyayyar kayayyaki, maimakon ace dole sai mutum ya rike kudi a hannun shi in zai je kasuwa domin siyayya.

Yana da kyau im mutum zai je cirar kudi yaje a sassafe, saboda mafi yawan bankuna suna loda kudi a ATM ne da misalin karfe 8 na safe, kashi kusan 3 cikin biyar na ATM ana musu lodi ne a irin wannan lokacin.

A dinga raba kafa wajen cire kudi, in mutum yana amfani da katin cirar kudi na bankuna biyu to don guje wa takurawa sauran masu cirar kudi sai ya tura kudin shi cikin dayan akant dinshi na banki, yadda zai je wani waje ya sake amfani da dayan katin shi na ATM.

Yafi dacewa mutum ya yi amfani da ATM din bankin da yake amfani da shi domin yanzu in ka sa katin ka a ATM din wani banki daban toh cire kudi mai yawa zai zame maka jidali saboda masu cirar kudi suna da yawa ba zai yiwu kayi ta cira ba, ba tare da mutane suna nuna damuwarsu da hakan ba.

Sannan dadin dadawa bankuna suna cajin Naira 65 in mutum ya cire kudi sau uku a ATM din bankin da bankin shi ba, wanda umarni ne da babban bankin Nijeriya ya kayyade.

Abu na gaba shine muddin mutum ya rude wajen amfani da ATM to ya yi maza ya neme taimakon masu gadin banki saboda gujewa bata lokaci a banza ba gaira ba dalili.

Kirga kudi a gaban ATM bata lokaci ne, saboda ATM a kayyade yake bada kudi don haka ba bukatar a tsaya a kirga, sannan hakan zai bata wa sauran jama’a da suke kan layi rai, sannan hakan ka iya jawo bata gari su sa ido akan mutum.

Kada ka bata lokaci wajen duba sauran kudin ka nawa a rage a akant saboda banki zasu turo maka sako ta lambar waya da yawan adadin kudinka da suka saura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here