Labarai

WASANNI: Amanju Pinnick Ne Sabon Shugaban NFF

Amanju Pinnick ya lashe zaben shugaban hukumar kwallon kafar Nijeriya wato NFF a zaben da aka gudanar a jiya  Talata a birnin Warri dake jihar Delta.

Pinnick mai shekaru 43, wanda shi ne kwamishinan wasannin jihar Delta, kuma shugaban kulob din Warri Wolves ya lashe zaben ne da kuri'u 32 daga cikin 44 da aka kada.

Abokin takararsa Dominic Iorfa ya samu kuri'u takwas, yayin da Taiwo Ogunjobi ya samu kuri'u hudu.
Shehu Dikko da aka yi hasashen zai iya lashe kujerar NFF janye wa ya yi daga takarar.

WASANNI: Messi Ya Zura Kwallaye Fiye Da 400 A Raga

Dan wasan Barcelona Lionel Messi, a karsheen makon da ya gabata ne ya zura kwallayensa na 400 a raga a matsayinsa na wanda ke bugawa a matakin kasa da kasa.

Messi dan asalin kasar Argentina ya zura biyu daga cikin kwallaye 6 a karawar da aka yi a ranar asabar data gabata  tsakanin Barcelona da Granada a gasar La Liga ta kasar Spain.

Kotu Ta Dage Yanke Hukuncin Karar Tsige Gwamna Murtala Nyako

Mai Shari'a Obong Abang na babbar kotun Lagos ya dage yanke hukuncin karar tsige tsohon Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako

Jama'a da dama sun hallara a wata kotun  birnin Legas a jiya  talata domin jin hukuncin da mai shari'a Obong Abang zai yanke akan karar da wani taliki ya shigar a madadin gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako da aka tsige, amma  sai alkalin ya dage yanke hukuncin.

Za Mu Yi Nasara Kan 'Yan Bindiga, Cewar Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan ya sha alwashin yin duk mai yiwuwa don ganin masu ayyukan ta'addanci a kasar ba su yi nasara ba.

A jawabinsa ga jama'ar kasar a kan cikar Nijeriya shekaru 54 da samun 'yancin kai, shugaba Jonathan ya ce gwamnati ta dukufa wajen tabbatar da tsaron dukkan jama'ar kasar ba tare da la'akari da inda suka fito ko addininsu ko kuma akidarsu ta siyasa ba.

Janar Buhari Ya Sanar Da Aniyarsa Ta Tsayawa Takara A 2015

Tsohon Shugaban Nijeriya Janar Muhammadu Buhari ya shaidawa magoya bayansa cewar zai tsaya takarar shugabancin kasar a shekara mai zuwa idan Jam’iyarsa ta tsaida shi a zaben shekarar 2015.

Yayin da yake jawabi ga kungiyoyin magoya bayan sa a babban birnin tarayya a Abuja, Buhari ya bayyana kalubalen da ke gaban Nijeriya yau a matsayin mai girma, inda yace matakin farko da ke gabansu shine raba wadanda suka kasa gudanar da mulki da mulkin kasar.

Jonathan Yana Amfani Da Addini Ne Wajen Wasa Da Hankalin Mutane - Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Lagos kuma jigo a jam'iyyar Adawa ta APC Bola Tinubu ya zargi shugaba Jonathan akan  amfani da addinine kawai wajen wasa da hankalin mutane domin cimma manufofinsa na siyasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar litinin da ta gabata  yayin ganawarsa da yayi da wadansu daga cikin ‘yan kungiya masu neman zaman lafiya a kasa a zauren Multi-Purpose LTV8 dake jihar Lagos.

 

 

Zamu Hukunta Atiku Da Jonathan - Hukumar Zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC  tace idan Jonathan da Atiku basu daina yin kampen din siyasa ba toh lallai zasu hukuntasu kamar yadda doka ta tsara.

Hukumar tace ba'a yarda wani yayi kampen ba har sai daga wata uku kafin zabe zuwa awa 24 kafin a kada kuri a.

Saboda haka ta umurci duk ‘yan takara dasu daina ko kuma su hadu da fushin hukumar.

Kamar yadda sakataran hukumar zaben Augusta Ogakwu ya bayyanawa manema labarai.

Me zakuce akan hakan?

Kotu Ta Yanke Wa 'Yan Boko Haram Uku Daurin Shekaru 75

Wata babbar kotun tarayya a Legas ta yanke wa wasu 'yan kungiyar Boko Haram uku hukuncin daurin shekaru 75 da aiki mai tsanani.

Mutanen uku da kotu ta samu da laifi, su ne:  Ali Mohammed, Adamu Karumi  da kuma  Ibrahim Usman, kowannensu zai shafe tsawon shekaru 25 a gidan yari saboda shiga kungiyar ta'addanci.

An gudanar da wannan shari'ah ce cikin sirri saboda bukatar kare rayukan shaidu.

Yau Nijeriya Ke Bikin Cika Shekaru 54 Da Samun 'Yanci

Muna taya dimbin masu karantamu murnan cikan Nijeriya shekara 54 da samun yan'cin kai.

TAMBAYA: Wane babban cigaba aka samu tundaga wannnan lokaci zuwa yanzu, kuma wace gwamnatine tafi kyau da kuma lalacewa?

Obasanjo Ya Sake Komawa Makaranta

 Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo na shirin komawa makaranta don samun babban digiri a fannin ilmin addinin Kirista.

 Duk da cewa tsohon shugaban kasan ya samu kwalin difloma a 2009, yanzu kuma yana shirin samun kwalin babban digiri, kamar yadda wani na kusa da shi ya bayyanawa  Premium Times.

 A yayin jin ta bakinsa, shi ma tsohon shugaban kasan ya tabbatar da hakan, inda ya ce yin hakan yana da matukar muhimmanci a gare shi domin zai taimaka masa wajen gudanar da ingantacciyar rayuwa,

Pages

 
 

Monthly archive