A cikin wani mummunan hari da suka kai da daddare, wasu ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun afka ƙauyen Gali da ke ƙaramar hukumar Alƙaleri a jihar Bauchi, inda suka sace mutane huɗu kuma suka kwashe kayan wasu shaguna guda biyar.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa harin ya faru da misalin ƙarfe 11:30 na daren Asabar, 19 ga watan Yuli.
- Bauchi Da Gombe Sun Koka Kan Jinkirin Aikin Haƙo Mai Na Kolmani
- Gwamnatin Bauchi Ta Fara Shirin Kirkirar Sabbin Masarautu Da Sarakuna Da Gundumomi
CSP Wakil ya ce ƴan bindigar, waɗanda suka zo da yawa sosai, sun fara farfasa shagunan ne kafin su tafi da masu shagunan zuwa wani wurin da ba a sani ba.
Ya bayyana sunayen waɗanda aka sace da suka haɗa da Tasi’u Malem Yahya, mai shekaru 32; Hakilu Ubayo, mai shekaru 15; Abdul Aziz Sulaiman, mai shekaru 28; da Rabiu Ganjwa, ɗan shekaru 16 — duk mazauna ƙauyen Gali ne.
Mai magana da yawun ƴansandan ya ce Kwamishinan ƴansandan jihar Bauchi, CP Sani Omolori Aliu, ya bayar da umarnin gaggawa ga DPO na Alƙaleri, tare da haɗa jami’an tsaro da masu gadin gari da mafarauta domin gano inda aka kai waɗanda aka sace da cafke waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp