Ƴan fashi sun sace fasinjoji guda bakwai a cikin motocin haya biyu a ƙauyen Eleyin da ke cikin ƙaramar hukumar Isin a Jihar Kwara.
A cewar rahoton LEADERSHIP, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:45 na yamma a ranar Juma’ar da ta gabata, lokacin da wasu ƴan fashi su biyar suka toshe hanya, suka tsayar da motoci biyu, sannan suka tilasta ɗaukar dukkanin fasinjojin zuwa wani wuri da ba a sani ba.
- Uwargidan Shugaban Kasar Sin Ta Tattauna Da Takwararta Ta Kasar Kenya
- Ra’ayin Matasa Kan Kungiyar ‘Yan Ta’adda Mai Suna Lakurawa Da Ta Fito A Kebbi
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa, daga cikin fasinjojin motar ɗaya, akwai shugaban sashin shari’a na ƙaramar hukumar Oke Ero, Barr. Elizabeth Arinde, da daraktan gudanar da ma’aikata na wannan ƙaramar hukumar, Alh. Musbau Amuda.
Kakakin Ƴansanda na Jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa an sami ceto fasinjoji biyu, Ganiyu Ajayi da Kolawole Adeyemi. Ta kuma ƙara da cewa, har yanzu ana ƙoƙarin ceto sauran fasinjojin guda biyar da kuma kama ƴan fashin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp