Daga Mustapha Hamid
Manomin mai suna Ijeh Chukwuedo, mazaunin Ubulu Ukun da ke Jihar Delta, yana can yana ƙoƙarin murmurewa bayan da Likitoci a Asibitin Federal Medical Center da ke Asaba su ka yi nasarar aikin tiyatar cire masa harsashi daga Cikinsa.
Manomin mai shekarun haihuwa 23, yana kan hanyar komawa Gida ne daga Gona, inda su ka yi kicibis da Dansandan mai suna Sajan Emeka, wanda yake cikin yanayi na mayen Giya, inda ya bude masa wuta a kan hanyar Ubulu-Issele-Uku.
Majiyar mu ta shaida mana cewa, Dansanda Emeka, tare da wasu abokan aikinsa su 2 suna ta neman Chukwuedo dan su kama shi a kan Kuɗin aikin jinga da ya karɓa har #15,000 daga hannun wani Mutum mai suna Funaya.
Jami’an tsaron, tare da Funaya sun ja tunga ne a bakin hanya, inda su ka yi dakon ɓullowan Chukwuedo daga Gonarsa.
Wakilin mu ya tattara mana bayanan cewa, Funaya yana hango ɓullowar Chukwuedo a kan Babur ɗin sa, sai ya yi maza ya ankarar da jami’an tsaron.
Jami’an tsaron sun yi yunƙurin tsayar da shi, amma sai ya ƙi tsayawa.
Yayin da suka ga ba za su iya cin masa ba, sai Emeka ya buɗe masa wuta, inda harsasai suka same shi a Cikinsa, da kuma Cinyarsa.
Wani maƙwabcin wurin da lamarin ya faru, wanda ya buƙaci da mu sakaya sunan sa, ya shaida mana cewa, a take cikin jini aka garzaya da Chukwuedo zuwa Asibiti, yayin da shi kuma Ɗansandan da ya yi harbin, aka kama shi.
Ya ci gaba da shaida mana cewa, “Sajan Emeka ya shahara sosai a wannan yankin namu wajen shan Giya, ko a ranar da ya buɗe wa Ijeh (Chukwuedo) wuta ma a cikin maye yake, su da kan su ‘yansandan da ke tare da shi sai da suka tuhume shi a kan dalilin da ya sa yayi harbin, jama’a sun harzuƙo sun so su ɗauki doka a hannunsu a lokacin, amma sai aka tseratar da shi, yayin da shi kuma Ijeh aka garzaya da shi zuwa Asbitin FMC da ke Asaba”.
Lokacin da wakilin mu ya je dan jin ta bakin Chukwuedo dai a ranar talata ya yi rashin sa’ar tarar da shi yana bacci.
Ya ci gaba da cewa, Funaya ya biya shi #15,000 Kuɗin aikin, amma sai ya ƙi ya ƙarasa aikin kamar yadda ainihi su ka yi yarjejeniya tun da farko.
Jami’in kare hakkin ɗan Adam ɗin ya shaida mana cewa, Funaya tare da rakiyar wani abokinsa mai suna Tochukwu sun je sun sami Chukwuedo ranar asabar kan cewa ya mayar masa da Kuɗinsa.
Gwamnishu ya ce, “an yi wani bikin al’adu ta ‘Iwu’ ranar Asabar a garin, Funaya da Tochukwu sun je har Gida suka sami Chukwuedo a kan ya mayar masa da Kuɗinsa, shi kuma ya ce ba zai mayar ba, saboda ya riga da ya fara aikin da su ka yi jingar, inda yayi masa alƙawarin cewa idan an kammala bikin al’adun zai je ya kammala masa aikin na sa”.
Ya ci gaba da cewa, “Tochukwu cikin fushi ya buƙaci Chukwuedo da ya mayar masa da Kuɗinsa, daga nan hayaniya ta fara a tsakanin su, inda Chukwuedo ke ganin Tochukwu na neman ya shiga sabgar da babu ruwan sa ne, daga nan suka fara ba hammata iska”.
“Washe gari sai Funaya ya jagoranci ‘yansanda dan su je su kama Chukwuedo, da suka je, sai suka tsaya a bakin hanya, suna jiran ya fito daga Gonarsa, lokacin da suka ga ya fito, sai su ka yi yunƙurin tsayar da shi”.
“Da yake hanyar ko yaushe ihun ka banza ne, ba a fiye samun giftawan mutane ba, shi kuma yana tsoron kar ko makasa ne, sai yayi ƙoƙarin arcewa, nan take ɗaya daga cikin ‘yansandan mai suna Sajan Emeka ya buɗe masa wuta, inda harsasai suka same shi a Cikinsa, da kuma Cinya, a take ragowar ‘yansandan suka garzaya da shi zuwa wani Asibiti da ke nan yankin, inda daga can Asibitin ne Likitoci suka buƙaci da a mayar da shi zuwa babban Asibitin tarayya FMC da ke Asaba, inda a can ne a ka yi nasarar yi masa tiyata, aka cire harsasan daga jikinsa”.
Gwamnishu ya shaida mana cewa, iyalan majinyacin sun kashe kuɗin da ya kai #50,000 a jinyar da su ke yi wa ɗan’uwan nasu, amma #10,000 kacal hukumar ‘yansanda ta aika musu da shi.
“ko sau ɗaya ba su taɓa zuwa dubiyar yanayin jikin nasa a FMC ɗin ba, yakamata Ɗansandan da ya harbe shin ya fuskanci hukunci daidai da doka, yana cikin maye, yanayin da bai kamata wanda yake ciki a ce yana ɗauke da Bindiga ba”.
Bayan da muka tuntuɓi Kwamishinan ‘yansandan Jihar, Zanna Ibrahim, ce mana ya yi, “ba ni da cikakken bayanin abinda ya faru amma zan bincika”.
Daga baya mun yi ta yunƙurin sake tuntuɓar nasa, amma duk lokacin da mu ka kira Wayarsa ba a amsawa.