Daga Mustapha Hamid
An dai gabatar da mutumin mai suna Abdullahi Sani, mazaunin garin Funtuwa ne a babban Kotun Majistare bisa zargin yi wa ‘yar ƙaramar yarinya ‘yar shekaru 3 kacal fyaɗe har sai da Allah Ya amshi ranta.
Wanda ake tuhumar mai shekarun haihuwa 50, an labarta mana cewa yana da ‘ya’ya har 7, kuma Gidansa yana maƙwabtaka ne da Gidan Yarinyar da ya yi wa fyaden.
Ya dai aikata wannan aika-aika nasa ne a ranar 12 ga Watan Oktoban 2017, inda bayan kama shi, aka tuhume shi da laifin yin kisan kai ƙarƙashin dokokin Penal Code shashi na 283, da kuma 221.
Alƙalin da aka gabatar da ƙarar a gaban sa tuni yayi umurni da a wuce da wanda ake tuhumar zuwa Gidan Sarƙa, har zuwa 18 ga Watan Satumba, inda za a cigaba da sauraran ƙarar.