ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙasashe 10 Da Suka Fi Samar Da Man Fetur A Duniya

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
Fetur

Yayin da ake ƙara nutsawa a cikin yaƙi tsakanin Amurka da Isra’ila da kuma Iran, ƙasashe masu samar da mai a duniya na ƙara zama wasu ƴan lele a idanun marasa man.

Hakan ya biyo bayan matakin da Iran ta ɗauka na rufe mashigar Hormuz wadda take iko da ita, wata mashiga da ake safarar kashi 20 cikin ɗari na man fetur da iskar gas da ake amfani da shi a duniya, kuma an samu raguwar man da ake bi da shi ta mashigar da kashi 95 cikin ɗari.

  • Ƙarin Farashin Man Fetur: TUC Ta Shawarci Gwamnati Ta Tallafawa Matatun Mai Na Cikin Gida
  • Matatar Dangote Ta Fitar Da Tan 456,000 Na Man Fetur Zuwan Wasu Ƙasashen Afrika

Wannan dai ya janyo tashin farashin man fetur da wasu dangoginsa da ake amfani da su kuma suke ratsawa ta mashiga, nauyin man Brent ya ta shi zuwa Dala 120 kamar yadda jaridar INN ta wallafa.

ADVERTISEMENT

Wannan ya sa BBC Hausa ta rubuta wannan maƙala domin nazari kan ƙasahen duniya 10 da suka fi samar da man fetur da sauran nau’o’insa a duniya.

 

LABARAI MASU NASABA

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Amurka – ganga miliyan 22

Sama da shekara bakwai a jere Amurka ce ke jan ragamar kasuwar duniya wajen fitar da man fetur, inda ta samar da sama da ganga miliyan 22 a kowacce rana.

Amurka a gefe guda kuma tafi kowacce ƙasa buƙatar man fetur ɗin saboda yawan al’ummar da take da su da waɗanda suke bayuwa zuwa ga yawan buƙatarsa.

Jihar Teɗas ce ke kan gaba cikin jihohin Amurka wajen samar da man fetur ɗin da kuma tazara mai nisa tskaninta da New Meɗico ta biyu, inda take samar da ninki uku na abin da New Meɗico ke fitarwa a kullum.

 

Saudiyya – ganga miliyan 10

Saudiya ce ƙasar da take samar da kimanin kashi 17 na man fetur da ake ajiyewa a matsayin na ko ta kwana a duniya.

Ita ce ƙasar da ta fi fitar da man fetur zuwa kasuwa duniya, tana samar da ganga miliyan 10.88 a kowacce ranar.

Wannan ya sa ta zama mai yanke makomar hukunce-hukunce da matakan da ake ɗauka a Ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta duniya OPEC.

A 2022, sai da ƙawar ta Amurka ta so ta ƙara yawan gas ɗin da take fitarwa kasuwar duniya domin sauƙaƙa farashi a kasuwar.

Rikicin Iran da Amurka da Isara’ila ya tilasta wa Saudiyya rage yawan man fetur ɗin da take samarwa daga miliyan 10 zuwa takwas, saboda rufe mashigar Hormuz da ake fitar da man fetur ɗin ta nan.

 

Rasha – ganga miliyan 10

Rasha ma na samar da ganga sama da miliyan 10 a kowacce rana, kuma tana ɓoye mafi yawan man fetur ɗin da take samarwa ne a West Siberia tsakanin tsaunikan Ural da ke yankin Urals-Ɓolga da kuma har zuwa wajen tekun Caspian domin faɗaɗa iko.

Yanayin kasuwanci ta ya fuskanci koma baya tun lokacin da ta fara yaƙi da Ukraine, Ƙungiyar Tarayyar Turai EU da ta ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziki a duniya G7 da kuma Australia sun sanya wa Rashan takunkumin fitar da man fetur ɗinta.

Gabanin fara yaƙin wajen shekarun 2021, ƙasashen turai ne ke sayan kimanin kashi 20 cikin ɗari na man fetur ɗin da Rasha ke samarwa, amma bayan fara yaƙin kason ya dawo kasa da 6.

China da India yanzu sune manyan masu sayan man fetur ɗin Rasha, inda suke sayan kashi kusan 92 na man fetur ɗin da Rasha ke fitarwa.

 

Canada – ganga miliyan 5

A 2024, yawan man da Canada take samarwa ya kusa ganga miliyan 6, inda take samar da ganga miliyan 5.997 a kullum, daga 237,000 da take iya samarwa a 2023.

Kusan duka rumbunan da take ajiye man fetur ɗin da take samarwa suna yankin Alberta.

Mafi yawan man fetur ɗin da Canada ke fitarwa tana fitar da shi ne zuwa Amurka, inda rahotanni suke ce a 2023 kashi 60 cikin 100 na abin da take samarwa ana shigar da shi Amurka ne, don an kwatanta da 2013 da Amurkan ke buƙatar kashi 33 kacal cikin 100.

Ana sa ran Canada za ta ƙara yawan man da take samarwa da ganga 140,000 a wannan watan na Afrilun 2026, a wani mataki na amfani da matatar ta garin Ottawa domin ƙara yawan man da ake samarwa zuwa ganga miliyan 23.6.

 

China – ganga miliyan 5

China na samar da ganga miliyan 5.33 a kowacce ranar bisa ga alƙaluman da aka fitar a 2024.

An yi ƙiyasin cewa China ce ƙasa ta biyu da ta fi buƙata tare da amfani da man fetur a duniya, a 2014 ta zama ta ɗaya da a wayan sayan man fetur a duniya.

Saboda yawan al’umarta da kuma haɓɓakar da tattalin arziƙinta yake yi a sannu, shi ya sa ta zama wacce ta fi buƙatar makamashi a duniya.

Ta zama ta ɗaya ne a duniya saboda tana shigar da mai ganaga miliyan 11 a kowacce ranar zuwa cikinta.

Kimanin kashi 70 cikin 100 na man da take saya tana karba ne daga kasashen da ke mambobin OPEC su Rasha Saudiyya da kuma Iraƙi.

Dan haka ba za a yi mamaki ba idan buƙatar makamashin China ta sauya kasuwar duniya, musamman a yanzu da aka rufe mashigar Hormuz.

 

Iran – ganga miliyan 4.5

Iran ita ce ƙasa ta shida cikin jerin ƙasashen da ke samar da man fetur, a 2024 yawan abin da take fitarwa ya kai ganga 4.62 a kowacce rana, wannan wani gagarumin ci gaba ne da ta samu, idan aka kwatanta da ganga miliyan 3.66 da take fitarwa a 2023.

Da wannan ƙarin da ta samu ta zama ta biyu cikin jerin ƙasashen ƙungiyar OPEC da ta fi fitar da man zuwa kasuwar duniya.

A cewar Hukumar bayar da bayanai kan makamashi EIA Iran ce ta uku a duniya da take da majiyin man fetur mai girma, ta biyu kuma wajen rumbun ma’adanin gas da ke ƙasa.

Mafi yawan man da ta fitar da ya kai ganga 1.4 a shekarar 2023 ta sayar da shi ne ga China.

Yaƙin da Iran ke yi da Amurka da Isra’ila ya sa ta rufe mashigar Hormuz mai muhimmanci, wata hanya da ake hada-hadar kashi 20 cikin 100 na man fetur da gas ɗin duniya ta cikinta.

 

UAE – ganga miliyan 4.5

Cikin sama da shekara 10 UAE ta kasance cikin manyan ƙasashen da suke samar da mai guda 10 a duniya.

Ƙasar da take cikin mambobin OPEC na samar da man fetur ganga miliyan 4.51 a mafi ƙaranci a kullum a shekarar 2024 kamar yadda rahotanni suka bayyana,

Ƙasar tana da wurin ajiyar rarar mai da zai ɗauki ganga bilyan 111, kuma mafi wayawan wuraren suna babban birninta Abu Dhabi.

A watan Mayun 2024 ne kamfanin mai na Abu Dhabi ya sanar da ƙarfin samar da ɗanyan man ƙasar zuwa ganga miliyan 4.85, yana cikin shirinta adadin ya kai miliyan biyar nan da 2027.

A cewar wasu rahotanni, hare-haren jiragen marasa matuƙa da aka riƙa kai wa kan manyan masana’antu da wurare masu mahimmanci da ke da alaƙa da kasuwancin mai da kuma rufe mashigar Hormuz ya ja UAE ta rage yawan man da take samarwa a kullum da kusan rabi.

 

Iraƙi – ganga miliyan 4.5

Ita ma wata mamba ce a OPEC, a 2023 tana samar da man da ya kai ganga miliyan 4.44 a kullum amma a 2024 sai aka samu ƙari duk da dai bai kai ya kawo ba.

A 2024 ne Iraƙi ta sauka daga matsayin mambar OPEc ta biyu da ta fi fitar da man fetur zuwa kasuwar duniya, inda Iran ta sha gabanta.

Bayanan da OPEC ta fitar a 2023 sun ce Iraƙi na da wurin ajiyar rarar mai da zai ɗauki ganga biliyan 145.02, wanda hakan ya kai kashi 11 na ma’ajin rarar da ake da shi a duniya.

Rikicin da ake yi tsakanin Iran da Isra’ila da Amurka ya janyo koma baya ga kasuwar man fetur din Iraƙi a watan Maris da ya gabata.

 

Brazil – ganga miliyan 4

Kasuwar man feturin Brazil a 2024 tana samar da ganga miliyan 4.28, kusan kowacce shekara ba a wani samun gagagrumin sauyi.

A cewa IEA buƙatar makamashin Brazil ta ninka cikin shekara 10 da suka gabata saboda bunƙasar tattalin arzikinta mai ɗorewa.

Inda ya fi ɗaukar kaso mai yawa na makamashin Brazil shi ne man fetur sai kuma ɗanyen mai da sannan gas da kuma lantarki.

A na sa ran Brazil za ta iya sama ta huɗu a duniya da ta fi fitar da mai kasuwar duniya nan da shekaru masu zuwa.

A 2024 man fetur ɗin ƙasar ya taimaka sosai wajen haɓɓakar safarar mai a duniya baki ɗaya.

 

Kuwait – ganga miliyan 2.78

Ta ƙarshe a cikin jerin ƙasashen da suke samar da man fetur ita ce Kuwait, wadda take samar da ganga miliyan 2.78 a kullum a 2024.

ƙasar ta yi ta fama wajen ganin ta dawo samar da ganga miliyan 3.5 saboda jan ƙafar da aka samu wajen saboda siyasar cikin gida.

Ɓangaren man ƙasar ne ke samar da kashi 50 na bunƙasar tattalin arzikinta a alƙaluman duniya, kuma da smaar mata kuɗin shhiga da ya kai kashi 90.

Ƙara samun wani man da aka yi a ƙasar ya ƙara bai wa ƙasar ƙwarin gwiwar haɓakar tatalin arzikinta a shekaru masu zuwa.

 

Wane matsayi Nijeriya take?

Nijeriya ce a matsayi na 11 cikin jerin ƙasashen duniya mafiya arzikin man fetur a duniya.

Wasu alƙaluma daga Hukumar Makamashi da Duniya, (EIA) ta fitara a 2024 sun nuna cewa ƙasar na da yawan man fetur a ya kai kimanin ganga biliyan 37 a ƙasa.

Ƙasar ce kan gaba a yawan arzikin man fetur da fitar da shia duniya, kodayake tana bayan Libya a wayan man da ke jibge a ƙarƙashin ƙasa.

Man fetur na Nijeriya – wadda mamba ce a ƙungiyar Opec, ta ƙasashe masu arzikin man fetur – na daga cikin na gaba-gaba mafiya inganci a duniya, don yake cikin mafiya daraja a kasuwar man fetur.

Fetur
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijar Ta Rattaba Hannu A Kan Dokar Haramta Auren Jinsi
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Za Mu Iya Sayar Da Manmu Ba Tare Da Wata Matsala Ba -Iran
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tabarbarewar Tsaro
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijeriya Ta Karbi Ƴan Nijeriya 268 Da Suka Tsero Daga Afirka Ta Kudu

MASU ALAKA

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
Labarai

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”
Ra'ayi Riga

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma
Labarai

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Next Post
Dawaki Sama Da 1,000 Za Su Fafata A Gasar Tseren Dawaki Na “Premie” A Kaduna

Dawaki Sama Da 1,000 Za Su Fafata A Gasar Tseren Dawaki Na "Premie" A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.