Hedikwatar Tsaro t Ƙasa (DHQ), ta ruwaito cewa manyan shugabannin ‘yan ta’adda, ciki har da Yellow Jambros, Alhaji Mallam, Ardo Idi (Alhaji Lawal), Lawal Kwalba, Salkado, Yellow Ibrahim, Gana’e, da Babangida, sun mika wuya ga sojoji a wannan makon.
Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, Janar Major Edward Buba, ya ce wasu ‘yan ta’adda suna ci gaba da nuna sha’awar mika wuya.
- An Samu Rarrabuwa Kan Yunƙurin Barin Damagum A Matsayin Shugaban PDP Har Zuwa 2025
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Raya Hanyoyin Karkara
Ya kara da cewa sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 135, sun kama 185, kuma sun ceto mutane 129 a wannan makon.
Hakazalika, sojoji sun kama masu satar man fetur 61 tare da kwato man da aka sace na kimanin Naira miliyan 889.
Janar Buba ya ce mika wuyan nasu ya biyo bayan sabbin hare-haren da sojoji kai wa ‘yan ta’addan, tare da hadin gwiwar al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya bayyana cewa sojoji sun kuma kwato makamai 113.
Makaman sun hada da bindigogi AK47 guda 72, bindigogin hannu guda 11, da bindigogin farauta guda 15, da sauransu.
A yanki na Neja Delta, sojoji sun lalata wuraren sarrafa man fetur na sata guda 82 da sauran kayan aiki.
Sun kuma kwato man fetur da aka sace lita 909,800.
Janar Buba ya yi alkawarin cewa sojoji za su ci gaba da nemo sabbin hanyoyi don magance matsalolin tsaro a kasar nan.