Ƙungiyar ƴan ta’adda ta IPOB ta yi fatali da hukuncin da babban kotun tarayya a Abuja ta yanke wa shugabanta, Nnamdi Kanu, na ɗaure shi har abada kan tuhuma bakwai da suka shafi ta’addanci. Kakakin IPOB, Emma Powerful, ya ce Kanu bai aikata wani laifi da dokar Nijeriya ta sani ba, inda ya bayyana cewa aiyukansa sun shafi neman ƴancin kai ne kawai, wanda doka ta duniya ke karewa.
IPOB ta soki yadda alƙalin kotun, Justice James Omotosho, ya yanke hukunci ba tare da la’akari da sashi na 36(12) na kundin tsarin mulki na 1999 ba, wanda ke cewa ba za a yanke hukunci ga wani laifi ba har sai dai idan an fayyace shi a rubuce. Ƙungiyar ta ce babu bindiga, ko bam, ko wani kayan yaƙi da aka samu a hannun Kanu, kuma babu wata shaida da ke nuna Kanu ya aikata laifi da dokar Nijeriya ko ta duniya ta sani.
- Alƙali Ya Sa An Yi Waje Da Nnamdi Kanu Saboda Rashin Ɗa’a A Kotu
- Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa
Ƙungiyar ta ƙara da cewa gwamnatin tarayya na la’akari da neman ƴancin kai a matsayin laifi, wanda a doka aka kare shi a sashi na 20 na kundin tsarin mulkin Afrika kan haƙƙin Ɗan Adam da ƴan ƙasa, da kuma dokokin ƙasa da ƙasa kan haƙƙin ɗan Adam. IPOB ta jaddada cewa neman ƴancin kai tsaye ba laifi bane, kuma yin kira ga gudanar da zaɓen a ware ba ɗaukar makami bane.
Haka kuma, IPOB ta ce rashin tsaro a Kudu maso Gabas ya ƙaru yayin da Kanu yake hannun hukumar DSS, inda rikice-rikicen da suka faru ba za a danganta su da shi ba. Ƙungiyar ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta sa ido a kan zaɓen a ware don samun ƴancin kan Biafra, tare da yin cikakken bayani kan laifuffukan kotu da take ganin an tauye haƙƙin dan Adam.














