Ƴan bindiga sun kai farmaki garin Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina, inda suka sace mutane da dama, ciki har da tsohon Darakta Janar na hukumar NYSC, Manjo Janar Maharazu Tsiga (ritaya).
Harin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na daren Alhamis, lokacin da ‘yan bindigar suka afkawa garin, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da tashin hankali.
- Yara 536,000 Ba Sa Zuwa Makaranta A Katsina – UNICEF
- Gwamna Radda Ya Samar Da Keke Napep Don Saukaka Zirga-zirga A Katsina
Rahotanni sun nuna cewa hukumomi sun samu labarin harin, kuma jami’an tsaro na ƙoƙarin ceto mutanen da aka sace.
Har yanzu ba a tabbatar da cikakken bayani game da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su ba, yayin da ake ci gaba da bibiyar lamarin.
Zamu ƙarin bayanai idan sun samu.