Bayan sa’o’i 28 da kammala taron zuba jari na Taraba (TARAVEST) da aka gudanar a Jalingo, wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai hari kan ƙauyukan Munga Lalau da Munga Doso na ƙaramar hukumar Karim-Lamido, inda suka kashe mazauna huɗu a ranar Juma’a.
Yayin da al’ummar ke iƙirarin cewa an kashe sama da mutane 30, ‘yansanda sun ce adadin waɗanda aka kashe ya kai hudu, yayin da dubban mazauna suka gudu daga ƙauyuka saboda tsoron kashe-kashe.
- Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga , Sun Ceto Fasinjoji 6 A Taraba
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 2, Sun Ƙwato Shanun Sata 1,000 A Taraba
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya kira taron tsaro a ranar Litinin 19 ga Mayu 2025, inda ya yi kira ga dukkan ɓangarorin da su daina rikici su koma gidajensu domin ci gaba da aikin noma.
Shugaban ƙungiyar matasan Munga, Malam Suleiman Joel, ya bayyana cewa maharan sun shigo ƙauyukan ne kan babura ɗauke da manyan makamai, suna kashe mutane a zazzage.
“Mun fitar da sanarwa kuma ta fito a wasu jaridu, muna kira ga gwamna ya zo ya ganin halin da muke ciki da idanunsa. Gwamnan ya gana da wakilanmu ya umarci waɗanda suka gudu da su dawo. Yanzu waɗanda suka dawo bisa umarnin gwamna an kashe su. Wane ɗan zuba jari ne zai zo ya saka hannun jari a cikin irin wannan zubar da jini?” in ji wani matashi daga Munga.
Gwamna Kefas ya yi Allah wadai da kashe-kashen, yana mai kira ga haɗin kai tsakanin al’umma da hukumomin tsaro.
Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, James Lashen, ya tabbatar da cewa an kashe mutane huɗu a harin, yayin da babu wani ɗansanda da ya jikkata a faɗan da suka yi da maharan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp