• English
  • Business News
Wednesday, October 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 2 Sun Sace 2 A Wurin Haƙar Ma’adanai

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
Bindiga

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari kan wani wurin haƙar ma’adanai da ke Oreke-Oke Igbo a jihar Kwara a ranar Laraba, inda suka kashe ‘yansanda biyu tare da yin garkuwa da ma’aikata biyu, ciki har da wani ɗan ƙasar China. Waɗanda aka kashe su ne ASP Haruna Watsai da Inspector Tukur Ogah, waɗanda ke aiki a rundunar 45 PMF da ke Abuja kuma aka tura su wurin don samar da tsaro.

Kamar yadda Jami’ar hulɗa da Jama’a ta rundunar ‘Yansanda ta Jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi ta bayyana, maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, inda suka bindige jami’an tsaron a kusa kuma suka tafi da bindigoginsu. Waɗanda aka sace su ne Mista Sam Xie Wie, wani ɗan ƙasar China, da Mista David Adenaiye, ɗan Nijeriya daga jihar Kogi. Dukansu suna aiki a wurin haƙar ma’adanan lokacin harin.

  • Sabon Shugaban Koriya Ta Kudu Ya Yi Alkawarin Sulhu Da Takwaransa Na Arewa
  • Kwararraun Likitocin Tiyata 6 Ne Kacal Suka Rage A Kano – Farfesa Sani

Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kwara, CP Adekimi Ojo, ya bayyana harin a matsayin mummunan abu, inda ya sha alwashin amfani da dukkan dabarun tsaro da bayanan sirri domin ceto waɗanda aka sace da kuma cafke waɗanda suka aikata laifin. Rundunar ta ce ana ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro da shugabannin al’umma don ƙarfafa tsaro da hana faruwar irin wannan hari a nan gaba.

An buƙaci mazauna yankin da su zauna lafiya kuma su kasance masu lura, yayin da ‘yansanda ke riƙon jama’a da su ba da sahihan bayanai da za su taimaka wajen ceton waɗanda aka sace da kuma gudanar da bincike. Rundunar ta kuma jaddada ƙudurinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar Kwara.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
Tsaro

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja
Tsaro

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22
Tsaro

Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22

October 12, 2025
Next Post
Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Ta’adda, Sun Kashe Wasu Da Yawa A Borno

Sojoji Sun Daƙile Harin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Wasu Da Yawa A Borno

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

October 22, 2025
Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

October 22, 2025
Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe

Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe

October 22, 2025
Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas

Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas

October 22, 2025
Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja

Gwamnoni Sun Yi Ta’aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Fashewar Tankar Mai A Neja

October 22, 2025
Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

October 21, 2025
Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

Sin Ta Kammala Ginin Cibiyar Adana Bayanai Mai Amfani Da Karfin Iska A Karkashin Ruwa

October 21, 2025
Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

Aikin Jinya Kyauta: Gwamnatin Zamfara Ta Kammala Zagaye Na 10 Na Kula Da Marasa Lafiya 3,447

October 21, 2025
Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

Ci Gaban Kasar Sin Ya Shaida Cewa Yawan Jama’a Ba Dalili Ne Na Rashin Ci Gaba Ba

October 21, 2025
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu

Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo

October 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.