‘Yan bindiga sun kai hari ga tawagar sojoji a ƙaramar hukumar Gudu ta Jihar Sakkwato, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji huɗu tare da raunata wasu biyu. Harin ya faru ne yau a kan hanyar Kukurau-Bangi.
Yahya Gudu, ɗan majalisar da ke wakiltar Gudu a majalisar dokokin jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa maharan sun ƙona motocin sintiri guda biyu na Sojojin.
- Yadda Aka Kashe Manoma 8 Da Sace Dabbobi 1,260 A Sakkwato
- Kwalekwale Ya Kife Da Fasinjoji 40 A Sakkwato
Gudu ya nuna rashin jin daɗinsa kan wannan al’amari, ya kuma bayyana cewa an sanar da Gwamna Ahmed Aliyu nan take, wanda ya sa a tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin da abin ya shafa.
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa ya ga ‘yan bindigar suna ratsawa ta yankin su a kan babura 20, kowanne ɗauke da mutane biyu masu makamai.
Da aka tuntube shi, ASP Rufa’i Ahmed, kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Sakkwato, ya ɗora alhakin amsa tambayoyi kan wannan lamari ga jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Soja ta 8, Laftanar Kanal Ikechukwu Eze, wanda ba a samu damar jin ta bakinsa ba a cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp