Kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya (TCN) ya sanar da wani hari da ya lalata kayan aikin layin wutar 330kV na Lokoja–Gwagwalada, wanda ya haifar da katsewar samar da wutar lantarki.
Wannan lamari ya faru ne a safiyar Asabar, 9 ga Nuwamba, 2024, inda masu lalata suka lalata turakunan wutar T306, T307, da T308, tare da sace wasu ƙarafa guda biyu daga layin.
- Da Ɗumi-ɗumi: DisCos Sun Sanar Da Sabbin Farashin Mitar Wutar Lantarki
- Gwamnatin Tarayya Da EU Sun Kulla Yarjejeniyar Bunkasa Wutar Lantarki
Injiniyoyin TCN sun yi ƙoƙarin mayar da wutar, amma ta sake yankewa, wanda bincike ya tabbatar da lalacewar kayan. Duk da haka, wutar tana ci gaba da ratsa ta layi na biyu yayin da TCN ke nemo kayan gyara don maye gurbin igiyoyin da aka sace.
Ndidi Mbah, babban manajan hulɗa da jama’a na TCN, ya nuna damuwa kan yawaitar irin waɗannan hare-hare da ke lalata kayan aikin lantarki a ƙasar. Ya jaddada cewa hare-haren baya-bayan nan, da suka haɗa da na Gwagwalada–Kukuwaba–Apo da Gwagwalada–Katampe, suna tsananta matsalolin samar da wuta a Nijeriya.