Ƴan bindiga sun kai hari a makarantar Government Girls Comprehensive Senior Secondary School (GGCSS), Maga, da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a Jihar Kebbi, inda suka kashe Mataimakin Shugaban makarantar, Hassan Yakubu Makuku, tare da sace wasu ɗalibai mata da ba a san adadinsu ba. Al’ummar yankin sun ce harin ya sake tayar da hankula a garin, wanda ke fama da yawan hare-hare a kwanakin nan.
Wani mazaunin Maga, Aliyu Yakubu, ya ce maharan sun shigo makarantar ne kimanin ƙarfe 5 na safiyar Litinin, ba tare da wata ƙwaƙƙwarar musayar wuta daga jami’an tsaro ba. Ya bayyana cewa harin ya jefa mazauna yankin cikin firgici da tashin hankali, abin da ya sa jama’a ke cikin tsananin damuwa da alhini.
- ’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi
- Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Yakubu ya ce sun harbe Shugaban Makarantar ne a lokacin da yake ƙoƙarin kare ɗalibansa daga faɗawa hannun ƴan bindigar. Ya bayyana rasuwar tasa a matsayin babban rashi ga makarantar da kuma al’ummar yankin gaba ɗaya.
Daily Trust ta rawaito cewa, a halin da ake ciki, babu wata sanarwa daga Rundunar ƴansanda Jihar Kebbi game da harin. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, bai amsa kiran waya da dama da aka yi masa ba yayin rubuta wannan rahoto.














