Wasu jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) guda uku da ke hanyarsu ta zuwa jihar Anambra domin shirye-shiryen zaben gwamna na ranar 8 ga Nuwamba, sun shiga hannun ‘yan bindiga a jihar Kogi.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa an yi garkuwa da jami’an ne a ranar Talata, a ƙauyen Aloma da ke ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
- Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC
- Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC
Sienna da suka ke tafiya da ita ya bayyana a cikin wani kiran waya cewa ƴan bindigar sun tare hanya, suka buɗe musu wuta, har suka lalata gilashin gaban motar, lamarin da ya tilasta musu tsayawa.
A cewar Direban motar, dukkan fasinjojin da ke cikin motar an yi garkuwa da su, ciki har da matarsa, baya ga jami’an INEC uku da kuma wasu fasinjoji uku da ke cikin motar da suke tafiya tare da su.













