Shugaban al’ummar Faruruwa a ƙaramar hukumar Shanono ta Jihar Kano, Alhaji Yahya Bagobiri, ya bayyana damuwa kan ci gaba da hare-haren ƴan fashi a garinsu duk da tura Sojoji da sauran jami’an tsaro a yankin.
Bagobiri ya yi wannan jawabi ne bayan wani sabon hari da aka kai a daren Lahadi, inda ƴan bindiga yaye kan babura suka mamaye garin Yan Kwada, suka sace mata masu shayarwa har biyar, sannan suka kwashe shanu kusan 50 da sauran ƙananan dabbobi. Wannan lamari ya jawo tsoro sosai a tsakanin mazauna yankin, inda ɗaruruwan mutane suka tsere daga garin don neman mafaka.
- Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi
- Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
Ya ƙara da cewa har yanzu hare-haren suna ci gaba kusan kowace rana duk da tura jami’an tsaro a yankin, inda ya ce: “Ko a jiya ma, an sanar dajami’an tsaro cewa ƴan bindiga suna tunkarowa, amma babu abin da aka yi. Suka zo da misalin ƙarfe 9 na dare, suka kai hari a gidaje, suka sace mata masu shayarwa.”
Bagobiri ya ce daga cikin matan da aka sace, ɗaya ta samu tserewa, yayin da mata hudu ke hannun ƴan bindigar. Ya kuma bayyana cewa an bar jariran matan a gida suna kuka ba tare da kulawa ba.
Shugaban ya roƙi Shugaba Bola Tinubu, mai ba da shawara kan tsaro na ƙasa (NSA) Nuhu Ribadu, da sauran manyan jami’an tsaro da su ƙarfafa ƙoƙarinsu wajen kawo ƙarshen waɗannan hare-hare, tare da ƙara tura jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.














