Gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da matakan korar ‘yan Nijeriya daga ƙasar, inda ake sa ran mutane 85 za su iso Lagos, yayin da wasu 116 ke tsare.
Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, ya bayyana haka yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, a Tafawa Balewa House da ke Abuja. Ya bayyana cewa waɗanda ke tsare a gidan yari a Amurka ne za su kasance cikin rukuni na farko na waɗanda za a dawo da su.
- Ya Kamata Amurka Ta San Ana Barin Halal Don Kunya
- Amurka Da Isra’ila Sun Sake Barazanar ‘Lugudan Wuta’ A Gaza
A nata ɓangaren, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu ta bayyana damuwa kan yadda ake gudanar da tsare-tsaren korar mutanen, inda ta buƙaci da a bi ƙa’idojin da suka dace na ƙasa da ƙasa. Ta jaddada cewa dole ne a samar da hanyoyin da za su rage raɗaɗin korar, musamman ga waɗanda ba su aikata wani laifi na tashin hankali ba.