Wasu waɗanda ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram ne sun yi garkuwa da tsohon jami’in hukumar shige da fice, Sheikh Gaji Maina Kara, da wasu fasinjoji biyu a hanyar Biu-Damaturu a jihar Yobe.
Majiyoyi masu inganci daga cikin dangin sun tabbatar da cewa harin ya faru ne da safiyar ranar Asabar a kusa da kauyen Kama.
- Babban Hafsan Sojan Nijeriya Ya Sha Alwashin Inganta Tsaro A Yobe
- Inganta Kiwon Lafiya: Gwamna Buni Ya Ziyarci Sashen Koyar Da Kwararrun Likitoci A Damaturu
Wani ɗan uwan wanda aka yi garkuwa da shi, wanda ya yi magana a sakaye, ya bayyana cewa tsohon jami’in ya dawo daga Mubi, jihar Adamawa inda ya ziyarci danginsa, lokacin da harin ya faru.
“Shi ɗan uwana ne, amma ba zan iya bayyana hakan a hukumance ba. Amma labarin ya yaɗu. Ina fatan hukumomin tsaro za su fitar da sanarwa nan ba da jimawa ba,”
in ji majiyar.
Wani shaida daga cikin dangin ya kuma shaida wa LEADERSHIP cewa direban motar ya bayyana cewa maharan sun yi musu kwanton ɓauna ne a lokacin da suke dawowa daga Biu zuwa Damaturu, inda aka yi garkuwa da fasinjojin uku.
Dangin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, da kuma ƙara tura jami’an tsaro zuwa yankin.
Harin ya zo ne a lokacin da ake samun ƙaruwar ayyukan ‘yan ta’adda a wasu sassan ƙasar, musamman a yankin Arewa-Maso-Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp