Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da harin bam da aka kai a ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya bayyana harin a matsayin ayyukan ta’addanci, yana mai bayyana irin matsin lambar da ‘yan ta’adda ke fuskanta sakamakon nasarar yaƙi da ta’addanci.
- Sallah: Tinubu Ya Buƙaci Haɗin Kai Da Sadaukarwa A Tsakanin ‘Yan Nijeriya
- Gaskiya Tsantsa Tinubu Ya Umarce Ni In Riƙa Faɗa – Ministan Yaɗa Labarai
Ya ƙara da cewa waɗanda ke da hannu a irin wannan tashin hankalin za su fuskanci shari’a kuma ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta hana ƙasar nan faɗawa cikin ruɗani.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa na ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron lafiyar al’umma. Ya kuma yi alƙawarin ƙara zage damtse wajen ganin an kawar da masu haddasa rikici da hargitsi a cikin al’umma.