ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sallah: Tinubu Ya Buƙaci Haɗin Kai Da Sadaukarwa A Tsakanin ‘Yan Nijeriya

by Sulaiman
2 years ago
Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar bikin Babbar Sallah, inda ya ce, bikin na nuni da sadaukarwa, ɗabbaka imani da biyayya ga nufin Ubangiji.

A wata sanarwa da mai ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, Shugaban Ƙasa ya taya al’ummar Musulmi murna tare da addu’ar Allah ya karɓa masu addu’o’insu da kuma ayyukansu na alheri.

  • Sojin Nijeriya Ta Musanta Zargin Cin Zarafin Matan Da Suka Tsira Daga Boko Haram
  • Tsadar Rayuwa A Babbar Sallah: Yadda Magidanta Ke Sama Wa Kansu Mafita

Haka kuma ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi tunani a kan maudu’in bikin, wanda ke da ma’ana mai ƙarfi da muhimmancin ga Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Ya jaddada cewa, sadaukarwa da aiki su ne muhimman sinadiran gina ƙasa, ya na mai cewa sai an yi nufi da aiki tare domin kawo sauyi mai girma.

Shugaban ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi wa ƙasar nan addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da yin aiki wajen inganta haɗin kai, zaman lafiya da cigaba.

LABARAI MASU NASABA

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Ya yi la’akari da sadaukarwar da ’yan Nijeriya su ka yi a cikin shekara ɗaya da ta gabata yayin da gwamnatin sa ta sanya ƙasar a kan turbar haɓaka da cigaba.

Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin sa na ba da fifiko ga tsaron lafiyar su ta jiki, ta zamantakewa da kuma tattalin arziki, ya ce ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba kan wannan kyakkyawan aiki.

Shugaban ya yi wa ‘yan Nijeriya fatan murnar bikin Sallah.

Tinubu
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Next Post
Ya Kamata Amurka Ta Cire Cuba Daga Jerin “Kasashe Masu Goyon Bayan Ta’addanci”

Ya Kamata Amurka Ta Cire Cuba Daga Jerin "Kasashe Masu Goyon Bayan Ta'addanci"

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.