Rundunar ƴansandan Nijeriya ta tabbatar da kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan wani ɗan ƙasar China mai suna Chen Wang, wanda aka tsinci gawarsa da raunuka da dama a ƙirji cikin ofishinsa da ke Ogere, jihar Ogun, a ranar 12 ga Janairu, 2025.
Wanda aka kama su ne Yunusa Abdullahi, ɗan shekara 25 daga jihar Borno, da Peace Keno Danlami, mace mai shekara 20 daga jihar Taraba. Rundunar ƴansanda ta ce an kama su ne a ranar 14 ga Yuli, 2025 a garin Jos, jihar Filato, bayan bincike mai zurfi da tsauraran matakai na sirri da aka gudanar tsawon watanni bakwai.
- FRCN Ya Kaddamar Da Shirin Koyar Da Sinanci Mai Taken “Hello China”
- China Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Trump Na Ƙarin Haraji Ga Kasashen BRICS
Mai magana da yawun rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa waɗanda ake zargin dukkaninsu ma’aikata ne a kamfanin WH Great Resource Ltd, kuma da dangantaka ta soyayya. An ce sun yi amfani da ɗaukewar ƙafa a ranar da abin ya faru don kashe na’urorin tsaro da kutsa cikin ofishin Wang, inda suka sace makullin gidansa kuma suka shiga gidansa suka yi fashi kafin su tsere daga jihar.
Rundunar ƴansandan ta ce an kama su ne bayan sun ɓuya a Jos suna amfani da sunayen bogi. Ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala gudanar da cikakken binciken.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp