Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta hana wani yunƙurin ‘hari da ‘yan bindiga suka kai kan jami’an NSCDC a kan hanyar Dutsinma-Kurfi a ƙaramar hukumar Dutsinma.
Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, 23 ga Fabrairu, 2025. Bayan samun kiran gaggawa da misalin ƙarfe 12:57 na dare, ‘yansanda daga ofishin Dutsinma suka gaggauta kai ɗauki, wanda ya haifar da musayar wuta da ‘yan bindigar.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Mutum Tare Da Sace Mutum Biyu A Kaduna
- Gwamnatin Katsina Ta Kashe Naira Biliyan 5.7 Wajen Sayen Awaki 40,000 Domin Raba Wa Mata
A sakamakon haka, ‘yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga, yayin da aka samu gawar ɗaya daga cikinsu a wurin. Jami’an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen bin sawun waɗanda suka tsere domin cafke su.
Rundunar ‘yansandan ta tabbatar da ci gaba da jajircewarta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp