Hukumar ‘Yansandan Jihar Plateau ta kama mutane uku da ake zargi da satar wayoyi a Jos da kewaye. Bisa ga bayanin daga Mr. Alfred Alabo, Jami’in hulɗa da Jama’a na ‘Yansanda (PPRO), an kama waɗanda ake zargin ne yayin da suke ƙoƙarin satar waya daga wani mazaunin yankin Rantya a ƙaramar kukumar Jos ta Kudu.
Alabo ya bayyana cewa waɗanda ake zargin, suna amfani da babur mai kafa uku wajen aikinsu, suna basaja a matsayin matuƙa baburan don kasuwanci saboda su ja hankalin waɗanda za su yi wa satar.
- Dubun Mai Garkuwa Da Mutane Ta Cika, An Yi Ram Da Shi A Jos
- Abin Da Ya Sa Muka Yi Zanga-Zanga A Kaduna -Masu Sharar Titi
A ranar 29 ga Agusta, da kusan ƙarfe 2:00 na rana, an kama waɗanda ake zargin a rukunin Rantya. A yayin da ake musu tambayoyi, sun amsa cewa suna daga cikin ƙungiyar da ke da kwarewa a satar wayoyi da sauran abubuwa a yankin Rantya. Ɓarayin sun amsa cewa suna amfani da dabaru daban daban wajen satar wayoyi da sauran abubuwa.
An samu wayar Android da babur mai kafa uku mai lamba PT 17437 daga hannun su. ‘Yansanda na ci gaba da binciken lamarin kuma sun yi kira ga jama’a su kasance masu lura da taka tsantsan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp