Jami’an ‘Yansanda a Katsina sun cafke wani ɗan damfara mai suna Bishir Abdullahi, wanda aka kama da katunan ATM guda 14 da ya sace, tare da zargin ya wawure sama da Naira miliyan ₦2.7 daga asusun bankunan mutane.
An kama shi ne a wani reshen bankin First Bank da ke Tudun Katsira, inda ya ƙware wajen sauya katunan ATM tare da cire kuɗin mutane ba tare da saninsu ba.
Kakakin Ƴansanda, Sadiq Abubakar, ya ce ɗan damfarar mai shekaru 37 ya yi amfani da katunan cirar kuɗin wajen warure kuɗaɗe da suka kai ₦49,000 zuwa ₦900,000 a lokaci-lokaci.
- ‘Yansanda Sun Karyata Jita-jitar Kai Harin Garkuwa Da Mutane A Jami’ar BUK
- CBN Ya Raba Lambobin Da Za A Yi Karar Bankunan Da Ba Sa Saka Kudi A ATM
Haka kuma, ‘yansanda sun sanar da wasu nasarori a fannin yaƙi da laifuka, inda suka cafke waɗanda ake zargi da satar kaya, garkuwa da mutane, da lalata kadarorin gwamnati.