Ana zargin wata ɗaliba a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano, da haɗa baki da saurayinta don kai hari kan wani malami mai suna Aliyu Hamza Abdullahi. Rahotanni sun ce ɗalibar ta fusata ne saboda ƙin amincewa da buƙatartq na sauya sashen karatunta.
A cewar Kakakin Kwalejin, Auwal Ismail Bagwai, ɗalibar ta isa ofishin malamin tare da saurayinta, inda suka ce masa ya kawo cikas ga yunƙurinta. Daga nan saurayin ya fito da adda ya kai wa malamin sara, wanda hakan ya sa ya samu rauni a hannayensa yayin da yake kare kansa. Ɗalibai a kusa sun yi sauri suka tsoma baki, wanda hakan ya sa maharan suka tsere.
- Tinubu Ya Ba Jama’an Tsaro Umarnin Kamo Ƴan Ta’addan Da Suka Kashe Mutane A Katsina
- SIMDA Ta Ƙulla Alaƙa Da Jami’ar Skyline Kan Ci Gaban Ilimi Da Kasuwancin Zamani A Kano
Malamin ya samu kulawar gaggawa a asibiti, yayin da jami’an tsaro na kwalejin suka kai samame gidan ɗalibar don cafke ta. Sai dai an ce ta tsere cikin gida, sannan wasu ƴan daba suka far ma jami’an tsaron da makamai.
A halin yanzu, ana cigaba da bincike kan lamarin yayin da ake neman ɗalibar da saurayinta, kuma malamin da aka kai wa hari yana cigaba da jinya a asibiti.