Tsofaffin daliban Sashen’ Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami’ar Bayero ‘yan shekarar 2015 sun sabunta Dakin Karatu na Sashen tare da gyaran wasu sassa na Sashen a Jami’ar.
A ranar Alhamis 02 ga watan Mayun 2024 aka gudanar da kasaitaccen bikin bude Dakin Karatu na Marigayi Farfesa M.A.Z Sani da tsofaffin daliban Sashen suka sabunta shi bisa jagorancin shugaban daliban na 2015, Alhaji Hassan Baita Ubawaru, wanda ya samu wakilcin Sakataren Kungiyar daliban, Muhammad Bashir Amin.
- Za Mu Sabonta Dakin Karatu Na Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero — Hassan Baita
- Jami’ar Bayero Kano Za Ta Karrama Sanata Barau Da Adesina Da Digirin Girmamawa
A nasa jawabin Shugaban Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami’ar Bayero, Dr. Jibril Shu’aibu Adamu, ya yaba da kokarin daliban ya kuma sanarwa da Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, irin kokarin da daliban suke yi na tallafawa Sashen, inda ya ce ko a kwanan nan tsofaffin daliban sun bai wa Sashen sababbin injinan nadar bayanan takardu uku tare da gyaran wasu sassa na Sashen.
A nasa jawabin, Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya yaba da kokarin daliban da irin tallafin da suke bai wa Sashen, ya kuma yi alkawarin ci gaba da tallafawa Sashen daga bangaren shugabancin Jami’ar.
Sagir ya ce, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya shi ne Sashe daya rak da ya fi kowane Sashen hulda da kasashen waje da suka hada da kasar Sin da Holandiya da Jamus da dai sauransu.
A jawabin shugaban daliban, Alh. Hassan Baita Ubawaru, wanda ya samu wakilcin Sakataren kungiyar daliban, Muhammad Bashir Amin, ya ce, za su ci gaba da tallafawa Sashen ta bangarori da dama, tare da aiki kafada-kafada da juna don ganin an inganta harkokin koyo d koyarwa da bunkasa Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa.
A nasa jawabin, Alh. Baita Ubawaru, wanda shi ne mahaifin shugaban daliban na 2015, kuma daya daga cikin wandanda suka tallafawa Shugaban Jami’ar wajen kaddamar da bude Dakin Karatun a yayin bikin, ya bayyana farin cikinsa tare da fatan Dakin Karatun ya zama mai amfanar da daliban Sashen da sauran al’umma baki daya.