• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ɗaliban Northwest Kano Sun Yi Zanga-Zanga Kan Ƙarin Kuɗin Makaranta

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
Kano

Ɗaliban Jami’ar Northwest da ke Kano sun gudanar da zanga-zanga biyo bayan ƙarin kuɗin makaranta da ya kai kusan kashi 200%, inda aka ɗaga kuɗin dadaga ₦19,700 zuwa ₦57,300 a sabuwar shekarar karatu ta 2024/2025. Wannan ƙarin ya haifar da fargaba a tsakanin ɗalibai da iyayensu musamman a yanayin matsin tattalin arziƙin da Nijeriya ke ciki.

Ƙungiyar Ɗalibai ta Jami’ar (SUG), a cikin wata sanarwa da shugaban ta, Abdussalam Mahmoud Ahmad, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa ta fahimci nauyin da ƙarin kuɗin ya ɗora wa ɗalibai. Ya ce “muna bibiyar duk wata hanya da za ta taimaka wajen neman mafita mai sauƙin da rage raɗaɗi,” duk da cewa ba su bayar da takamaiman lokacin da za a warware lamarin ba.

  • Sanatocin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar ‘Yan Wasan Kano
  • Ma’aikatar Tsaron Kasar Sin Ta Maida Martani Game Da Munanan Kalaman Sakataren Tsaron Amurka Kan Kasar Sin

Wannan ƙarin kuɗin ya ƙara tayar da ƙura a tsakanin ɗalibai da iyayensu duba da yadda farashin karatu ke ci gaba da tashi a jami’o’i a faɗin ƙasar. Ɗalibai da dama sun bayyana fushinsu a kafafen sada zumunta, musamman a X (Twitter), inda aka fara amfani da taken #NWUFeeProtest.

Izuwa yanzu, ba a ji wani bayani daga mahukuntan jami’ar ba dangane da dalilin wannan gagarumin ƙarin kuɗin lokac guda. Ƙungiyar Ɗalibai ta buƙaci a kwantar da hankali, tare da buƙatar dalibai su gabatar da ƙorafinsu kai tsaye zuwa ofisoshin ƙungiyar dake harabar Muhammadu Buhari Way Main Campus ko Ado Bayero House City Campus.

Wannan rikici ya ƙara bayyana yadda matsin tattalin arziƙi da rashin fayyace manufofi ke ci gaba da kawo cikas ga tsarin ilimi a Nijeriya, inda ɗalibai ke fama da ƙarin kuɗin makaranta da kuma ƙarancin tallafi daga hukumomi.

LABARAI MASU NASABA

Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260
Manyan Labarai

Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

October 28, 2025
gaza
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato
Manyan Labarai

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
Next Post
Jirgin Sojoji Yayi Kuskuren Buɗe Wuta Kan Ƴan Sa Kai A Maru

Jirgin Sojoji Yayi Kuskuren Buɗe Wuta Kan Ƴan Sa Kai A Maru

LABARAI MASU NASABA

Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

October 28, 2025
Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

October 28, 2025
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

October 28, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

October 28, 2025
Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

October 28, 2025
An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

October 28, 2025
Gwamna Bago Ya Amince Da Biyan Karin Albashin Naira 20,000 Ga Ma’aikata 

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi

October 28, 2025
Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

October 28, 2025
Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15

Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15

October 28, 2025
gaza

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.