ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jirgin Sojoji Yayi Kuskuren Buɗe Wuta Kan Ƴan Sa Kai A Maru

by Abubakar Sulaiman
1 year ago
Sojoji

A ƙalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai tare da farmakin wani jirgin saman Sojin Nijeriya da aka tura domin kawo ɗauki. Al’ummar yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari a ƙauyen Mani da rana, inda suka buda wuta kan manoma da ke aikin gona tare da sace fiye da mutane 50.

Shaidu sun ce jirgin saman Sojin da aka turo domin kawo ɗauki ya buɗe wuta a kan ‘yan sa kai da sauran mutanen yankin da ke ƙoƙarin kai ɗauki, har wasu daga cikinsu suka rasa ransu. Wani da ya tsira daga harin jirgin ya bayyana cewa: “Da muka hango jirgin sama, sai ya fara harbi. Mun kwanta kasa muna yin kamar ya bugemu kafin muka samu damar tserewa.”

  • Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 60 A Borno
  • Sojoji Sun Koka Bisa Jinkirin Yanke wa Ƴan Ta’adda 1,450 Hukunci

Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan mummunan kuskure daga Sojojin ke faruwa ba. Sun ce ‘yan bindigar sun yi barazanar dawowa, yayin da suka roki gwamnati da ta ƙara tura jami’an tsaro tare da horar da su wajen tantance maƙiya daga fararen hula domin gujewa irin wannan asara.

ADVERTISEMENT

Rahoton BBC Hausa ya bayyana cewa a watan Janairu 2025, jirgin saman Sojojin Nijeriya ya hallaka mutum 16 a ƙauyen Tungar Kara, yayin da wani hari a watan Disamba 2024 ya kashe fararen hula 10 a jihar Sokoto – lamarin da gwamnoni suka bayyana a matsayin harin kuskure. Har yanzu rundunar Sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan sabon harin na Maru ba.

Yayin da matsalar tsaro ke kara tsananta a Zamfara da sauran jihohin Arewa maso yamma, jama’a na ci gaba da buƙatar ɗaukar matakin gaggawa daga gwamnati, musamman wajen samar da ƙarin tsaro, da kayan aiki na zamani da ingantattun dabarun yaƙi da ‘yan bindiga domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

LABARAI MASU NASABA

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

Sojoji
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su
  • Abubakar Sulaiman
    Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya
  • Abubakar Sulaiman
    Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso
  • Abubakar Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Next Post
Za A Samu Mamakon Ruwan Sama Da Hazo Daga Litinin Zuwa Laraba A Nijeriya

Za A Samu Mamakon Ruwan Sama Da Hazo Daga Litinin Zuwa Laraba A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Sojoji

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Sojoji

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
Sojoji

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.